Mafi yawan samarin da ke nuna ra’ayi kaina, kuɗina suke so ba ni ba, inji jarumar barkwanci Ashmusy

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Shahararriyar ‘yar wasan barkwanci Ashmusy, ta bayyana cewa, kaso mai yawa na samarin da ke matsowa wurinta da sunan soyayya sun zo ne su yi kuɗi da ita.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da ita, inda ta faɗi hakan a matsayin dalilin da ya sa har yau ba ta da saurayin da za ta iya kira da masoyinta.

Sannan ta ƙara da cewa, a nata ra’ayi za ta so ta samu saurayin da yake da abin yi, yake amsar albashi kowanne wata, amma fa ba wanda ya fi ta samu ba. Ma’ana dai wanda ba zai yi kwaɗayin ya so ta don abinta ba, don yana da abinda ke shigo shi, sai dai abinda yake samun bai kai wanda ita ta ke samu ba.

By Editor