Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Wakilai ta fusata kan rashin halartar hafsoshin tsaro da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a wani zama na mu’amala da aka shirya gudanarwa a jiya Alhamis yayin zaman majalisar.
A maimakon haka dai shugabannin tsaro sun tura wakilai.
A makon da ya gabata ne dai majalisar ta shirya muhawara a sassa daban-daban da shugabannin tsaro yayin da take shirin yi da sauran sassan ƙasar.
Biyo bayan wani tanadi da kundin tsarin mulki ya bayar na mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, majalisar ta ƙi amincewa da wakilcin shugabannin tsaro, maimakon haka ta ɗage zaman.
An sake ɗage zaman zuwa ranar Talatar mako mai zuwa kamar yadda majalisar ta dage cewa dole ne shugabannin hafsoshin su bayyana a muhawarar.
Hafsan hafsoshin su ne Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojoji (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Babban Hafsan Sojan Sama (CAS), Air Marshal Hassan Abubakar da Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa (CNS), Vice Admiral Emmanuel Ogalla.
