Babu wanda ya saci kuɗi a Nijeriya kamar Diezeni – TY Ɗanjuma

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon babban hafsan sojin ƙasa, Theophilus Ɗanjuma, ya yi zargin cewa tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke ta yi fice wajen cin hanci da rashawa.

Ɗanjuma ya ce Alison-Madueke ita ce mace ɗaya tilo a Nijeriya da ya sani da ta yi fice wajen cin hanci da rashawa.

Ya yi magana ne a lokacin da yake ƙaddamar da cibiyar lafiya ta Goodwill Medical Center (GMC) a Umuchigbo, Iji Nike a ƙaramar hukumar Enugu ta Gabas, ranar Talata.

A cewar tsohon hafsan sojojin, Diezani ta kafa tarihin da har yanzu babu wanda ya buge ta.

Ya ce, “na kasance ina cewa idan kana son a yi wani abu yadda ya kamata a kawo a kan lokaci ba tare da wani uzuri ba, ka bai wa mace aikin, har muka samu ministar man fetur mace.

“Matar ta yi fice a cin hanci da rashawa. Ta kafa tarihin da har yanzu babu wanda ya doke shi.

“Don haka, ina cikin nazarin bayanina lokacin da na haɗu da wata mata mai suna Farfesa Uche Amazigo. Ni da Uche mun yi nisa sosai wajen shawarwari.

“Haduwa ta farko da Uche ita ce a tsakiyar watan Oktobar 2010 lokacin da ta samu rakiyar Misis Franca Ilamiji, wata ‘yar ƙabilar Igbo.

“Na buƙaci ta dawo gida Nijeriya domin bayar da tata gudunmawar wajen ciyar da ƙasar gaba, amma sai na tuna ta’adin da Madueke ta yi sai inji cewar bai kamata ta dawo yanzu ba sai komai ya daidaita,” inji shi.

By Editor