Babu dimukraɗiyya a Nijeriya

Spread the love

Daga NAFIU SALISU

Idan a na batu na mulkin Dimokraɗiyya da alfanunta a ƙasashen da suke tafiyar da ita Dimokraɗiyyar, to za mu iya cewa ba za a taɓa saka ƙasata Nijeriya ba, domin babu ita a jerin ƙasashen da suka cancanci a kira ‘yan ƙasar masu rayuwa a ƙarƙashin mulkin Dimokraɗiyya. Wannan kuma ta faru ne dalilin rashin tafiyar da dimokraɗiyyar a yadda take, da kuma tsarin da ake tafiyar da ita a ƙasa.

Dimokraɗiyya dai ita ce, Gwamnatin al’umma domin al’umma, wato Gwamnatin da al’ummar ƙasa suka kafa domin ita kanta al’ummar don rayar da mutane su ci muryar Gwamnatin da suka kafa. Don haka a cikin Gwamnatin farar hula ta Dimokraɗiyya, akwai ‘yanci da walwalar jama’a kamar yanda kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba kowanne ɗan ƙasa dama a sashi na 39, da sauran abubuwa da suke tabbatar da Dimokraɗiyya a cikin ƙasa.

Ba Dimokraɗiyya ba ce yin ƙarfa-ƙarfa a kan ‘yan ƙasa (talakawa) da ko ma waye, kamar yanda muke gani a yanzu a ƙasarmu Nijeriya. Ɓangaren tsaro ya zama tamkar wasan kwaikwayo, kotuna da Alƙalai sun zama tamkar ‘yan shirin fim da mai ba da umarni, ‘yan majalisu sun mayar da kujerunsu qahon zuƙar jinin al’ummar ƙasa. Mulkin Dimokraɗiyya ya zamo mulkin kama-karya, damarka ta ɗan ƙasa ta faɗin albarkacin baki ma ta gagara ka faɗa saboda hakan zai iya zamo maka barazana da salwantar rayuwarka, haƙƙinka na ɗan ƙasa da za a baka wajen inganta rayuwarka ya zamo ba a bakin komai ba, kuma ka yi magana wanda ke cikin ruwa ya ce ka tayar masa da ƙura.

Idan Dimokraɗiyya ake yi a Nijeriya, mene ne dalilin da zai sa wakilan al’umma suka tare a Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja? Don wasu tunda suka ci zaɓe suka watsar da yankunansu da jama’ar da suka zaɓe su, suka manta da su, suka manta tsayuwar da suka yi a cikin rana, suka ɓata lokacinsu wajen bin dogon layi don su kaɗa musu ƙuri’a. A irin wannan lokacin wasu ko abincin da za su ci a gidajensu ba su da shi. Me ya sa ‘yan majalisu ba za su tsaya a yankunan da suke ba tare da al’umma su rayu tare suna ganin abinda ke zuwa ya dawo, sannan su tashi don su magance musu matsalar a matsayinsu na wakilansu? Shin sai sun zauna a Birnin Abuja ne za su iya yi wa talakawa aiki? Ko kuwa dai ana fakewa ne da guzuma don a harbi karsana?

Idan dimokraɗiyya a ke yi a Nijeriya, me ya sa ake yi wa gaskiya bi-ta-da-ƙulli, ana yaƙarta da ƙarfin tsiya domin ƙarya ta rinjaye ta? Mun ga yadda faɗin gaskiya yake zamowa ƙalubale ga wanda yake faɗarta, kamar gidajen Radiyoyi da jaridu, mujallu da kafar sadarwa ta yanar Gizo (Internet). Idan Aikinka shi ne faɗa shugabanni don a tabbatar da gaskiya a yaƙi ƙarya, to ka zamo abokin adawarsu. 

Ko shakka babu ‘yan siyasa a Nijeriya sun lalata Dimokraɗiyya, sun ɗaiɗaitata, sun mayar da ita tamkar kayan gado da mutum zai gada a gidansu. Shi ya sa za ka ga cewa gurvatattun ‘yan siyasa ba sa abota da mutanen kirki da za su iya faɗa musu gaskiya, hakazalika su ne masu tara ‘ya’yan talakawa da basu da galihu su mai da su karnukan farauta a lokacin zaɓe, da zarar sun cimma muradunsu na ɗarewa karagar mulki kuma, to shikenan sai su watsar da su saboda an ci moriyar ganga an ya da kwaurenta.

To ta ina za a kira wannan da sunan dimokraɗiyya? Ka lalata ‘ya’yan al’umma amma kai ka inganta rayuwar naka ‘ya’yan, ka koyar da ‘ya’yan al’umma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, kai kuma naka ‘ya’yan ka koyar da su jin daɗin rayuwa. Ka tara musu kuɗi a Bankunan ƙasa da na wajen ƙasa, ka saka su a makarantun kuɗi masu tsada, ka siya musu abin hawa mai tsada, ta ko’ina ba ka yarda su ravi talaka, kuma wannan talakan shi ne wanda ya zaɓe ka, ko yake zaɓarka don ka hau kujerar mulki ka gina rayuwarsa, amma bayan ya zaɓe kan sai ka juya masa baya ka ke gina rayuwar ‘ya’yanka da danginka. Yanzu wannan shi ne Dimokraɗiyya?

Mu kalli yadda aka gudanar da zaɓukan Kano, Zamfara, Plateau (Jos) da jihar Nassarswa cikin tsafta da tazarar ƙuri’u masu rinjaye, amma ƙiri-ƙiri kotu ta fito ta bayyana cewa duk Gwamnonin da suka ci zaɓe ta rushe zaɓensu. Bayan kafin hakan kowa yana da jam’iyyarsa da ya tsaya takara a cikinta, sannan kafin zaɓen ya fita yawon neman amincewar jama’a (Campaign), sannan aka zo aka zave shi, aka yi ƙirgen ƙuri’u, aka ware marasa kyau da masu kyau aka tantance, ga shaidu don tabbatar, shaidun kowacce jam’iyya.

Bayan haka, shugaban hukumar zaɓe mai alhakin sanar da wanda yayi nasara ya fito ya faɗa, aka tabbatar da nasarar wanda ya ci, sannan aka zo aka yi bikin rantsuwa har aka gama aka je matakin da Gwamna zai fara ayyuka a jiharsa, amma wai daga baya a zo a ce an rushe wannan nasarar tasa, anya kuwa akwai adalci a cikin wannan lamarin? Tabbas dai akwai lauje a cikin naɗi.

Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya na jam’iyyar adawa ta PDP wato Alhaji Atiku Abubakar ya yi wata magana da kuma maganar tasa tana kan hanya, cewar da ya yi Gwamnatin APC a Nijeriya tana amfani da qarfin mulki wajen ƙoƙarin murƙushe jam’iyyun hamayyar ƙasar nan. Ko shakka babu wannan magana haka take, domin masu iya magana sun ce “Biri ya yi kama da mutum”, kuma ido ba mudu ba ya san kima. Misali: Ba wani abu ba ne ya sa suke ƙoƙarin kawar da Gwamnatin Kano mai ci ta Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ba sai don shirinsu na ganin sun sake wucewa a zaɓe mai zuwa na 2027, wannan shi ne kawai. Don Kano ta kasance babban garin da kowanne ɗan siyasa zai so samun ƙuri’ar mutanen Kano a zaɓen shugaban ƙasa, wanda rasa ƙuri’ar mutanen Kano zai iya zamo wa babban ƙalubale ga kai wa matakin nasara ga duk wani ɗan siyasa dake zawarcin kujerar Shugaban ƙasa a Nijeriya. 

Su waɗanda suke tayar da jijiyar wuya a kan sai sun cire Gwamnan Kano a kan kujera sun ɗora wanda suke so, shin sun manta halin da gidajen marayu ke ciki a jihar Kano? Ko sun manta halin da asibitoci da makarantu ke ciki a jihar Kano? Mutane suna cikin ƙuncin rayuwa da rashin kwanciyar hankali, yunwa da fatara amma su ƙoƙarinsu kawai su ƙwaci mulki da ƙarfin tsiya. Ba su damu da me zai faru ba a garin yin hakan, ba su damu da rayukan da za su iya salwanta ko shiga cikin uƙuba ba a yayin yin hakan, su kawai kujerar suke buƙata ko da al’ummar Kano za su fuskanci uƙuba.

Akwai abinda ya faru a lokacin da nake aiki a ɗaya daga cikin gidajen Radiyo a Kano, wanda yana ɗaya daga cikin muhimmin abin da ya sa na yi wannan rubutu, domin abu ne da ba zan tava mantawa da shi ba. A lokacin Gwamnatin APC an yi abinda jama’ar Kano ba za su manta ba wato kalmar nan ta (Inconclusive) da suka ce ma’anarta shi ne zaɓe bai kammalu ba. Wanda ya san lokacin da hakan ta faru ya san me aka yi, an yi duk wata maƙarƙashi da tuggu haɗi da makirci don murɗe zaɓe a Kano, an yi amfani da ‘yan daba da wasu jami’an tsaro marasa kishi wajen cimma wannan muradin.

A wancan lokaci an yi ƙoƙarin farmakar gidan Radiyon da nake aiki a Kano, don kawai an faɗi abubuwan da aka riƙa yi na ta’addanci a rumfunan zaɓe, wanda abokan aikina da dama sai da aka farmake su a lokacin da suke ayyukansu na ɗaukar rahoto a wurare daban-daban a jihar Kano, amma Allah ya tsallakar da su. Akwai wanda aka fasa masa waya mai tsada, aka biyo wata za a kashe ta ta tsira da kyar, da wanda aka biyo ya faɗa motarsa yana ƙoƙarin tserewa aka rufe shi da jifa aka farfasa masa gilas ɗin motarsa ya sha da kyar. An yi wa ‘yan jaridu da dama irin wannan a lokacin da ake yin wancan wasan kwaikwayo zagaye na biyu da aka ba shi suna da ‘inconclusive’.

Sannan abinda ya ƙara tabbatar mana da cewa an shirya kawo farmaki a gidan Rediyon namu a wancan lokaciv shi ne, kawo mana jami’an (Mobile Police) da aka yi a sirrance aka girke a wani ɓangare na cikin gidan, wanda idan ba mu ma’aikatan gidan ba babu wanda zai san cewa akwai jami’an tsaron da suke tare da mu don ba mu kariya, kuma ba Gwamnati ce ta ba mu ba, hasali ma ba ta san da su ba in ba daga baya ta sani ba ta hanyar ‘yan leƙen asirinta.

To bayan an sanar da Gwamnan da yake kai cewa shi ya sake cin zave, ranar Litinin mun fito aiki da safe ba zan manta ba, sai ga jami’an tsaro na soja sun zo gidan Rediyo a cikin motoci da sunan sun sami labarin za a kawo hari gidan Rediyon ne suka kawo ɗauki, amma sai Allah ya sa babu abinda yake faruwa a dai-dai lokacin, wanda mu kuma muka kalli lamarin da cewar, ko dai su waɗanda suka shirya attack ɗin sun ga babu nasara kuma asirinsu zai tonu suka fasa, ko kuma dai sun ga cewar hakan ba zai haifar musu da ɗa mai ido ba.

To irin wannan shugabancin shi ne za a kira da Dimokraɗiyya a Nijeriya? Zai fi dacewa dai da mulkin-kama-karya. Domin har yanzu talakan Nijeriya bai san mene ne romon Dimokraɗiyya ba, don ‘yan siyasar da yake rayuwa a tare da su ƙoƙarin tsotse jinin jikinsa suke yi ba wai inganta lafiyarsa ba ta yadda jinin jikin nasa zai ingantu ya yi rayuwar farin ciki ba.

Mu kalli yadda a kwanakin nan aka jefa wa masu taron mauludi bom a wani ƙauye dake cikin ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, wanda kuma sojojin Nijeriya ne suka yi wannan muguwar aika-aika, sannan har a fito a ce an yi hakan ne a bisa rashin sani? Rashin sanin mutanen ƙauye da suke taron mauludi ko kuwa rashin sanin su waye ‘yan bindiga? Idan har jami’an tsaron soji suka kasa tantance ɗan ta’adda da mutanen da gari da ba ‘yan ta’adda ba, to ta ya ya za su iya yin faɗa da ‘yan ta’adda har su magance matsalar tsaro a ƙasa? Ko kaɗan wannan bai yi kama da kuskure ba, ganganci ne da aikata kisan gilla ga farar hula da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

‘Yan ta’addar nan an san su an kuma san wuraren zamansu a cikin daji, sannan su ba a ƙafa suke yawo ba, suna tafiya ne a kan Babura duk inda za su je, kuma kowanne za ka gan shi ɗauke da bindigarsa AK47 a jikinsa, sannan kowanne mashin zaka samu yana ɗauke da mutum uku goye a baya, kayan jikinsu babu farare ko mai launin haske sai duhu. To ta ya ya zaka haɗa masu taron mauludi da waɗannan mutanen da kodayaushe suna cikin kaya mai duhu. Masu taron mauludin nan ba a kan ababen hawa suke ba, kuma ba ɗauke suke da makami ba.

Sannan uwa-uba suma suna rayuwa ne a cikin matsi da takurar ‘yan bindiga, amma aka je aka jefa musu bom. To tambayar a nan ita ce, da sunan ‘yan ta’adda aka jefa musu bom bayan basa ɗauke da kowanne irin makami, ko kuwa dai an yi niyyar kashe musulmi ne a lokacin da suke gudanar da wani taronsu da suka saba yi a cikin tsarinsu na raya wani abu da suke yi a cikin addininsu? Wanda kuma kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba su damar yin hakan? Irin wannan abin shi ne Dimokraɗiyya? Idan har haka ne, don me za a ce akwai Dimokraɗiyya a Nijeriya?.

A rayuwar da muke yi a yanzu, ɗan Nijeriya ba shi da tabbacin ya ya makomarsa za ta kasance a hannun ‘yan siyasa da masu mulki, domin juya shi ake yi tamkar sitiyarin mota, tamkar waina a cikin tanda. Babu wani talakan Nijeriya da yake yin bacci a cikin salama da kwanciyar hankali a yau, saboda me? Saboda yana fama da tsadar rayuwa, irin su: Tsadar abinci, tsadar suttura, rashin tsaro, rashin lafiya, ba ilimi, ba ya samun magani kyauta a asibitin Gwamnati, babu sauƙi a rayuwa domin masu abin hawa ma suna ajiyewa saboda man da za su zuba yana gagararsu.

A ƙauyuka suna fama da ‘yan bindiga, waɗanda suke azabtar dasu da muzguna musu, yin garkuwa da mutane da neman kuɗin fansa, kisan gilla da fyaɗe ga mata, cin zarafin ƙananan yara, fashi da makami a gida ko a hanya. Duk waɗannan munanan abubuwa ne da suka fi faruwa a kan talakan Nijeriya, amma shugabanni sun fi buƙatar kasancewarsu a kan kujerunsu na madafun iko a kan samun kwanciyar hankalin al’ummarsu. Haka-zalika, damuwarsu ta lokacinsu yafi bayuwa ne ga lamuran kawunansu na yin abinda suke so a lokacin da suka ga dama.

Don haka batun cewa ana yin Dimokraɗiyya a Nijeriya wannan ba gaskiya ba ne, zai fi kyau idan aka danganta hakan da kama-karya, domin al’ummar Nijeriya (musamman yankin Arewa), babu irin uƙubar da ba ayi mana. A gidajenmu ba ma barci cikin nutsuwa, a kasuwanninmu ba ma gudanar da cinakayyarmu cikin nutsuwa, ba mu da ikon bin hanyoyin motarmu don yin balaguro ba tare da fargaba ba, ba mu da ikon zuwa ƙauye mu yi noma cikin kwanciyar hankali. A hanya fargaba, a kasuwa haka, a cikin gida ma babu nutsuwa. Kullum al’amura ƙara rikicewa da rincavewa suke.

Da wannan kuma shugabanni suke ta buga sharholiya da bulayinsu, sun yi watsi da al’umma suna fagamniya da layi gami da faɗi-tashi ba don sun sha kayan maye ba, sai don rashin nutsuwa da kwanciyar hankalin da suka rasa a dalilin rashin cin moriyar Dimokraɗiyyar da ake mulkarsu a ƙarƙashinta. Da wannan nake kiran al’ummar Nijeriya kan lallai mu gane cewa da ruwan ciki a ke jan na rijiya, kuma tilas abar wa ɗari ƙwansa. Mu san inda yake mana ƙaiƙayi mu sosa, mu tashi tsaye don yin yaƙi da waɗannan alamura. 

Nafiu Salisu marubuci ne kuma manazarci mai sharhi a kan al’amurra yau da kullum musamman na siyasa da haƙƙoƙin talaka. Ya rubuto daga jihar Zamfara, [email protected], [email protected], waya: 08038981211, 09056507471

By Editor