Ƙasashe 153 sun marawa Gazawa kan Yahudawa

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kwanaki da makonni wataqila ta kai ga watanni a na cigaba da ruwan boma-bomai kan al’ummar Gaza da ya biyo bayan wani hari da ‘yan HAMAS su ka kai kan yankunan matsunan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan Yahudawa ko mazauna Isra’ila. Haƙiƙa mafiya yawan duniya na ba wa Falastinawa gaskiya da nuna sun daɗe su na shan azaba a hannun Isra’ila kai tun ma kafa Isra’ila a yankin su a 1948.

Ukubar da Falastinawa ke sha ta sa zuciyar yawancin su ta bushe da daina ɗaukar mutuwa a matsayin abun tsoro. Yaro Bafalastine kan iya tasowa cikin rugugin bindigogin Isra’ila da ma hare-haren jiragen saman yaƙi. Za ka tarar da matsahin Bafalastine ya na rayuwa ba tare da abokan sa na wasan kasa ba don zai yiwu sojojin Isra’ila sun kashe su ko wasun su na gidajen yari. Akwai waɗanda Isra’ila ke cafkewa tun su na da bakin gashi har sai sun yi farin gashi a gidan yari.

Abun dubawa a nan duk wanda a ka sako daga gidan yari ba ya nuna sanyin guiwa ko firgita da za ta sa shi nadamar matakan da ya ɗauka na kare muradun Falastinu na mallakar ƙasar kan ta. Misalin irin mutanen Isra’ila a watan Janairu ta sake ɗaya daga Palastinawan da ya fi kowanne daɗewa a gidan yari mai suna Karim Younis bayan kammala ɗaurin shekaru 40.

Younis dai yanzu mai shekaru 60 ya fara zaman ɗaurin ne bayan samun sa da laifin hallaka wani soja Bayahude mai suna Avraham Bloomberg a 1983 a tuddan Golan da Isra’ila ta mamaye bayan yaƙin nan na 1967, inda Yahudawa ƙarƙashin Firaminista Levi Eshkol kafin Firaministar su ta mace Golda Meir ta karba a 1969 su ka ci galaba kan ƙasashen Larabawa.

Younis dai duk da Bafalastine ne ya na yankin ƙasar Isra’ila ne don akwai Larabawa kashi 5% na al’ummar Isra’ila waɗanda kuma duk dangin Falasɗinawa da su ka zaɓi zama a Isra’ila bayan ƙirƙiro ƙasar a 1948.

Tuni ministan cikin gida na gwamnatin Isra’ila mai tsaurin ra’ayi Aryeh Deri ya rubuta takarda ga ministan shari’a ya na buƙatar a cirewa Younis rigar kasancewa ɗan Isra’ila.

A ƙauyen su Younis, ‘yan uwa, abokai da sauran jama’a sun ɗauke shi a kafaɗa su ka yi ta zagawa tituna da shi su na yi ma sa kirarin kasancewa jan gwarzo da ya sadaukar da kan sa ga gwagwarmayar ‘yancin Falasdinawa.

Karim Younis ya nuna farin ciki ga abun da ya zayyana gudunmawar da su ka bayar ta kare ‘yancin Falasdinawa ya na mai cewa su na shirye da ba da karin gudunmawar ta wannan fuska. Ko ma a fursunonin da isra’ila ta sako don karɓar mutanen ta da HAMAS ta kama akwai matasan da ba mamaki in ba don irin wannan dalili ba za su yi ta zama a gidan yari har sai sun kai tsufan Younis ko ma fiye in ma rai bai yi halin sa ba. Daukar mataki ma na yajin cin abinci da wasu Falasɗinawa ke yi a gidan yarin Isra’ila ihun ka banza ne don ba ya sa a sako su ko yi mu su wani sassauci.

Gaskiyar magana Yahudawa ba su ɗauki Falasɗinawa da wata daraja ta ɗan-adam ba ma balle har su amince da barin su, su kafa kasa mai babban birni a gabashin birnin Ƙudus.

A bara ma yankin Falastinawa ya adka cikin matukar juyayi biyo bayan bindige shahararriyar ‘yar jarida Bafalastiniya Shireen Abu Akleh da sojojin Isra’ila su ka yi. Marigayiyar na aiki ne da sashen Larabci na gidan talabijin Aljazeera.

Sojojin na Isra’ila sun harbi Shireeen Abu Akleh a ka a daidai sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin. An san Shireen da jajicewa cikin aikin da ta yin a tsawon shekaru 25 kuma ta kan ɗauko rahotanni daga yankunan da a ka gallazawa Falastinawa don fito da gaskiyar yanayin da a ke ciki.

Da farko Isra’ila ta so shashantar da kisan da nuna harsashi ne da ya yi batan kai daga Falastinawan wajen musayar wuta ya kashe ta. Daga bisani babban hafsan sojan ƙasar Laftanar Janar Aviv Kochavi ya dawo daga batun da nuna ba tabbas na yadda ‘yar jaridar ta mutu kuma Isra’ila ta yi nadamar afkuwar hakan.

Amurka ta nuna takaicin kisan Shireen da zayyana kisan da murƙushe ‘yancin ‘yan jarida.

Shireen Abu Akleh ta shahara a labarun da ta kan bayar kan uƙubar da Falasɗinawa ke sha a hannun Isra’ila.

Hatta editan marigayiyar wato Ali Samoudi ya samu rauni bayan harbin sa da a ka yi a gadon baya amma ya na samun sauƙi a asibiti. Tun bara da wannan kisan gilla ya afku zuwa yanzu ba wani hukunci ko Allah wadai da a ka yi da waɗanda su ka yi kisan.

Ba mamaki shaharar labarin mutuwar ta ma don ita ‘yar jarida ce da babbar kafar labaru. Irin waɗanda a ke kashewa a wannan yanayin a kan iya kala mu su zargin su na yunƙurin kai hari ne ko a na zargin su na ɓoye da wuƙa ko bindiga a jikin su.

Ƙasashe 153 cikin membobin babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya 193 sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da dakatar da buɗe wuta nan take kan Gaza.

Ƙuri’ar dai ta biyo bayan buƙata ce daga ƙungiyar ƙasashe Larabawa da kuma ta haɗin kan ƙasashe Musulmi don ɗaukar matakin da zai rage tinƙahon kwamitin tsaro na majalisar da ya kaɗa ƙuri’ar da Amurka ita kaɗai ta hau kujerar naki.

A nan ɗin ma ƙasashen sun yi fama da Amurka da Austria duk da ba a amince da matsayar ƙasashen biyu da ke son a zayyana HAMAS da mummunan suna da kuma yin tir da ita ba; wato kamar a ce ƙungiyar ta’addanci ne don haka duk inda a ka gad an HAMAS a ka hallaka shi kawai.

An kuma samu ƙasashe 10 da su ka kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da dakatar da yaƙi a Gaza inda ƙasashe 33 su ka ƙaurace wa kaɗa ƙuri’ar gabaɗaya don ba sa so a ga su na marawa kowane ɓangare baya.

Kaɗa ƙuri’ar ba za ta zama wajibi a dakatar da buɗe wutar ba amma ta nuna ƙasashen duniya masu rinjaye ba sa marawa yadda Isra’ila ke amfani da jiragen yaƙi da manyan bindigogin atilare wajen ragargaza Gaza da jama’ar ta.

Gabanin nan Amurka ta yi amfani da damar ta, ta hawa kujerar naki wajen hana karɓar ƙuri’ar kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya don tilasta dakatar da buɗe wuta da Isra’ila ke yi kan Gaza.

Ƙasashe 13 cikin 14 sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da dakatar da buɗe wutar inda Burtaniya ta kaucewa kaɗa ƙuri’ar.

Ministan wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da ke jagorantar Larabawa ya garzaya don gamsar da Amurka ta amince a dakatar da buɗe wutar amma buƙatar ba ta samu karɓuwa ba.

Wakilin dindindin na Amurka a majalisar Robert Wood dama ya ce Amurka ba za ta yarda da hakan ba don zai iya ba wa Hamas damar shirya yaƙi na gaba ne kuma ya yi kafar angulu da yunƙurin kafa ƙasar Falastinawa a gefe da ta Yahudawa.

Wood ya ce rashin sako matan da Hamas ke garkuwa da su ya wargaza cigaban yarjejeniyar tsagaita yaƙin.

Da alamu Isra’ila za ta ƙara matsa ƙaimin ƙudurin ta na murƙushe dukkan ‘yan Hamas kafin janyewa daga yakin.

Sai dai a yadda Hamas ko Falastinawa su ke ba za su daina yaƙi don murƙushewa ba sai dai ko duk za su kare a doron ƙasa.

Zuwa ƙarshen makon jiya sojojin Isra’ila sun kashe mutum dubu 17, 487 a Gaza a cigaba da ruwan wuta da su ke yi kan sassa da dama.

Tun wargajewar yarjejeniyar tsagaita wuta, Isra’ila ta cigaba da ruwan boma-bomai hatta a sassan da a ke amfani da su a matsayin tudun mun tsira ko wajen kwashe fararen hula.

A wani hari kan Khan Younis, Isra’ila ta kashe Falastinawa 6 inda can ma a Rafah da ke kan iyaka da Masar, Isra’ila ta kashe mutum 5.

Falasɗinawa da ƙungiyar HAMAS sun yi Allah wadai da yadda Amurka ta hau kujerar naki a majalisar ɗinkin duniya wajen kaɗa ƙuri’ar tsagaita wuta.

Har yanzu ƙasashen Larabawa da sauran ƙungiyoyin agaji na kira ga samun tsagaita wutar don dakatar da zubar da jinin waɗanda ba su yi wa kowa laifi ba.

Sojojin Isra’ila sun buɗe wuta a ɗakunan asibitin Kamal Adwan a Gaza inda hakan ya zama babbar barazana ga jarirai 12 da a ke kulawa da su a ɗakin yara.

Kakakin ma’aikatar lafiya a Gaza Ashraf Qudra ya baiyana harbe-harben Isra’ila da ya haɗa har da wasu sassan asibitin.

Qudra ya ce su na fargabar rayuwar yaran don an raba su da samun madara da kuma na’urar taimakon rai.

Hakanan Qudra ya ce sojojin Isra’ila da su ka zagaye asibitin sun kama shugaban asibitin Ahmad Al-Kahlot da sauran ma’aikata su ka tsare su da hana su ruwa da abinci bayan gana mu su azaba.

Kammalawa;

Yaƙin da Isra’ila ta ke yi na murƙushe ‘yan HAMAS ya hallaka fiye da mutum 17,000 kuma kiraye-kirayen tsagaita wuta don shigar da kayan tallafi ya ci tura. Ko me za a ce ƙuri’ar da ƙasashe 153 su ka kada ya nuna tausayawa Falasdinawa da nuna fin ƙarfi ba zai ɗore ba har abada. Duk tsananin yaƙi da za a yi dole wataran sai an zauna don yin sulhu kuma bakin bindiga bai taɓa zama kashe wutar rikici bakiɗaya ba.

By Editor