Kotun Ƙoli ta ɗage yanke hukunci kan zaɓen Gwamnan Kano

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ƙoli ta ɗage yanke hukuncin zaɓen gwamnan Kano zuwa wani lokaci da ba ta ambata ba.

Zaman da Kotun ta yi mai alƙalai biyar a ranar Alhamis, ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro.

A ranar 17 ga Nuwamban 2023 Gwamnan Kano, Abba Yusuf da Jam’iyyarsa ta NNPP suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli inda suke ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke nasarar da Gwamna Abba ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ran 19 ga Maris.

Kazalika, jam’iyyar ta nusar da Kotun Ƙolin dambarwar da ta auku a hukuncin baya inda kotu ta tabbatar da nasarar Abba tare da neman a biya shi diyyar Naira miliyan ɗaya saboda ɓarnar da aka yi masa.

Alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara ne suka tabbatar da nasarar Nasir Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Kano.

Alƙalan sun yanke cewa Yusuf na Jam’iyyar NNPP ba shi da rijista a matsayin cikakken ɗan Jam’iyyar wanda ya sa bai cancanci tsayawa takara ba.

Sai dai a dogon zaman da Kotun Ƙolin ta yi a ranar Alhamis, ɓangarorin sun yi ƙorafin ko kotu na da hurumi game da matsayin zama mamban mutum a wata Jam’iyya.

Haka nan, lauyoyi sun tafka muhawara game da yiwuwar kotu ta sake waiwayar laifin da INEC ta tafka na rashin rataɓɓa hannu kan takardun ƙuri’a na Jihar Kano.

By Editor