Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta’aziyya dangane da rasuwar dattijon kasa, Ambasada M.Z Anka, tare da bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Zamfara.
A ranar Juma’a Allah Ya yi wa marigayin cikawa.
Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fada cikin sanarwar da ya fitar ran Juma’a cewa, Gwamna Lawal ya ce rasuwar Ambasada Anka ta haifar da wagegen gibi saboda kwarewarsa.
A cewar Gwamnan, “Ba ahalin Ambasada M.Z Anka kadai ke alhinin rasuwarsa ba, har ma da al’ummar Jihar Zamfara baki daya.
“Marigayi Anka ya yi rayuwa abar koyi, mai cike da kyawawan dabi’u da gaskiya da kuma kwazo. Ya isa hujja rawar da ya taka wajen kirkiro Jihar Zamfara da kuma jajircewarsa wajen ganin jama’arsa ta cigaba.
“Ambasada Anka nagartaccen jagora ne, mai dora jama’a kan turbar da ta dace, kuma mabubbugar farin cikin jiharmu.
“A madadin Gwamnatin Jihar, muna mika ta’aziyya ga iyalai da daukacin Masarautar Anka dangane da rasuwar marigayin.
“Muna roko Allah Ya gafarta kurakuransa, Ya sanya Aljannah Firdaus makoma gare shi.”
