Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Dan wasan gaban Uruguay Luiz Suarez ya koma Inter Miami ta da ke aasar Amurka, inda zai sake haduwa da tsoffin abokan wasansa na Barcelona Lionel Messi, Sergio Busquets da Jordi Alba.
Suarez, wanda shi ma ya lashe kofunan lig da Nacional da Ajax da kuma Atletico Madrid, ya zura kwallaye 17 a wasanni 33 yayin da Gremio ta kare a matsayi na biyu a gasar Seria A ta Brazil a kakar wasa ta 2023.
Bajintar dan wasan na daga cikin abin da ya sanya aka zave shi a matsayin gwarzon dan wasa a gasar.
Amma kwantiragin shekaru biyu da ya kulla da Gremio a 2022 ya kare da wuri saboda Suarez ya ji ba zai iya sake buga wani cikakken wasa a Brazil ba sakamakon matsalar ciwon gwiwa da ya samu.
Miami mallakar tsohon kyaftin din Ingila David Beckham ta kulla yarjejeniya da Messi, Busquets da Alba a 2023, kuma ‘yan wasan uku sun taimaka wa qungiyar lashe kofi na farko da gasar kofin League a watan Agusta.
Suarez, wanda ake yi wa kallon daya daga cikin ’yan wasan gaba a zamaninsa, ya lashe kofunan La Liga hudu a Barcelona tare da Messi, Busquets da Alba tsakanin 2015 zuwa 2019.
Dan wasan ya kasance wani vangare na kungiyar Barca da ta lashe gasar zakarun Turai da kuma gasar kofin duniya ta FIFA a 2015.
’Yan wasan na Miami dai sun taka rawar gani a karkashin jagorancin tsohon dan wasan Ingila Phil Neville, wanda aka kora a watan Yuni, kafin dawowar Messi.
