Sauyin yanayi: Ƙalubalen da wasu garuruwa ke fuskanta a Jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Rahoton da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya ta fitar a 2019 ya bayyana cewa Nijeriya ta na asarar kimanin fili mai fadin murabba’in kadada 350,000 a duk shekara, sakamakon yadda hamada ke ci gaba da mamayewar yankuna, wanda hakan ya na faruwa ne ta musababbin sauyin yanayi, mai alaka da ayyukan yau da kullum da Dan Adam masu jawo dumamar yanayi.

A nata bangaren, a wani sabon binciken da Hukumar Agora Policy ta gudanar a wannan shekara (2023), ta bayyana cewa, Nijeriya za ta iya yin hasarar Dalar Amurka kimanin biliyan 460 sakamakon sauyin yanayin da duniya ke fuskanta, nan da shekarar 2050 mai zuwa, matukar ba ta dauki ingantattun matakan kan-da-garki ba.

Jihar Yobe tana daya daga cikin Nijeriya masu fuskantar matsalolin gurgusowar hamada mai alaka da sauyin yanayi, al’amarin da yake da alaqa da sha’anin tsarin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu, wanda ya dace a samu sauyin da za su taimaka wajen rage dumamar yanayin da canjinsa. Haka kuma, sakamakon tasirin sauyin yanayin ya na shafar yankuna da al’ummar jihar kai-tsaye, wanda yake zama babbar barazana ga ci gaba da yanayin rayuwar mazauna yankunan.

Bugu da kari kuma, yankunan kananan hukumomin Yunusari, Yusufari, Geidam, Bade, Karasuwa, Machina, Bursari, da Tarmuwa a jihar Yobe, su na daga cikin sassan jihar wadanda suke dandana kudarsu a hannun sauyin yanayin, kuma babbar barazana ga mazauna yankunan.

Wakilinmu a jihar Yobe ya tattauna da Mallam Baba Alkali, Sakataren karamar hukumar Yusufari, a jihar Yobe, ya bayyana cewa sakamakon sauyin yanayin, yankunansu na fuskantar karancin ruwan sama, savanin shekarun baya, wanda ya jawo tangardar noma da abinci ga al’ummar yankin.

Ya qara da cewa, wannan jinkiri da aka samu na samun ruwan sama kan kari, babban abin damuwa ne, musamman ga manoma wadanda sama da kaso 70 cikin dari sun dogara da noman damina, al’amarin da ya jawo koma baya ta fuskantar noma abinci.

Malam Baba ya nanata cewa, qarancin itatuwa a yankin ya na daya daga cikin matsalolin yankin; saboda yadda wadannan bishiyoyi suke kasancewa kariya ga gonaki da gidajensu daga mamayar hamada, tare da guguwar mai karfin gaske, musamman a lokacin hunturu da farkon damina.

“Wannan ya jayo al’ummar mu ke rayuwa cikin yanayin karancin abinci, rashin ayyukan yi, da zaman kashe wando. Garuruwa da dama ne ke fama da mamayewar rairayin hamada a gidaje da gonakin noma a shekaru da dama da suka gabata.

‘’Saboda a lokacin da wasu yankuna dake kudancin jihar Yobe ke samun ruwan sama ga damina, a yankunanmu qura tare da iskar guguwa mai tsananin gaske muke fama da ita. Har damina ta yi nisa mu na baya.

“A haka har dole ta sa manoma cire tsammani wajen samun damina mai kyau da zasu girbi amfanin gona mai yawa, savanin sauran sassa, sakamakon karancin ruwan sama, wanda aka fara shi a makare. Wanda ya sa amfanin da muke nomawa; gero, dawa, ridi da maiwa da makamantan su basu samu ba kamar yadda muka saba a wannan damina ba.”

A nashi bangaren, Lawanin kauyen Gremadi, Alhaji Maidala Zanna, ya ce hata mafi yawan hanyoyin su na mota zuwa kauyukansu rairayin hamadar ya mamaye, wanda hakan ya sanya ba kowace mota zata shiga kauyukan ba.

‘’Mamayar yashin hamadar ya yi tsanani fiye da kowane lokaci a sanin da muka yi, saboda a shekarun baya rairayi ya mamaye kashi 10 ne cikin dari na gonakinmu, amma yanzu ya bar mana 40 ne kawai muke iya shuka amfanin gona, sauran kashi 60 din duk yashi ne ya nutsar dasu.”

Ya ce, “A cikin wannan kashi 40 cikin dari, kashi 25 ne kawai na noman amfanin gona, kashi 15 kuma na kiwon dabbobi ne, amma ko wannan fili da muka bar shi don kiwo, wasu Fulani daga jamhuriyar Nijar sun mamaye shi don kiwon dabbobinsu kuma sun hanamu sakat a matsayinmu na ‘yan kasa. Shima wannan wani babban kalubale ne garemu.”

“Wannan kakkarfar guguwar mai dauke da dusar kura ta na ci gaba da mamaye wa da lalata gidajenmu masu yawan gaske a yankunanmu. Haka kuma, yanzu haka da nake magana da ku katangar gidana ta rushe a karo na uku, sakamakon wannan bala’i na zaizayar hamada.”

‘’Bugu da kari, abin bai tsaya nan ba, ya rutsa da wasu makwabtana, hamadar ta nutsar da gidansu dole sun koma wasu unguwanni a cikin gari; gidaje ne gasu nan birjik wadanda ba za a iya kirgasu ba, wanda hamada ta binne tare da yashi kamar yadda kuke gani.’’ Inji shi.

Wakilinmu ya lura da cewa sakamakon dumamar yanayi da sauyin yanayi, guguwar yashi da kura sun rivanya, al’amarin da ya jawo karancin ruwan sama a wannan yankin, inda ya janyo farin da ake samun hatsaniya tsananin makiyaya da manoma a duk shekara.

Malam Ahmed Abubakar masani kan sauyin yanayi, ya ce jihar Yobe na daya daga cikin jahohin da ke kan gaba, wadanda ke makwabtaka da jamhuriyar Nijar, masu fuskantar kalubalen gurgusowar hamada sakamakon iskar kasurwar arewa maso gabas mai karfin gaske.

Ya kara da cewa, ‘’Yobe ta na cikin Jihohi 19 da ke kan gaba kan matsalolin gurgusowar hamada masu iyaka da Jamhuriyar Nijar, yanki ne wanda yake kan gaba a hamadar Sahara.”

“Sannnan kuma a koda yaushe al’amarin ya na yin tasiri ne sakamakon wannan sauyin yanayi wanda ya hada da iska mai dauke da kura mai gusar da rairayi, sakamakon guguwar da ke tasowa daga kasurwar Arewa Maso Gabas.

‘’Don haka duk lokacin da wannan iskar ke tasowa ta wuce a kusan watan Nuwamba zuwa Maris a kowace shekara, muna fuskantar matsalar kura mai karfin gaske, ta na haifar da gurgusowar hamada a gurare da dama tare da kawo matsaloli daban-daban ga yankuna tare da al’ummar wadannan yankuna.”

Ya ce, mafita daya wadda ta dace wajen magance wannan matsala, ita ce dashen itace masu yawa a kowane lungu da sako. Ya ce, dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shirin dashen itatuwa na ‘Great Green Wall’ wanda shirin ya na da nufin gina katafariyar gandun bishiyoyi a kowane bangare na kasar nan. Wanda shi ne zai baiwa muhallinmu kariya daga mummunar illar gurgusowar hamada.