Jagora ya yaba wa Hamisu Ibrahim kan rubuta littafin koyar da Larabci da Turanci

Manhaja logo

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Kwamared Adam Abubakar Adam wanda aka fi sani da Jagora, daya daga cikin jagororin Kungiyoyin Ci Gaban Al’umma a Karamar Hukumar Nasarawa Jihar Kano ya yaba wa hazikin marubucin nan Malam Hamisu Ibrahim wanda ya bada gudunmawa wajen rubuta littafi wanda ya kunshi kalmomin Larabci zuwa Turanci domin amfanin masu son koyon Larabci tun daga tushe kamar dai yadda Jagoran ya bayyana cewa wannan ba karamin aiki ba ne da zai taimaka wa wadanda suka san Turanci su koyi Larabci a matakin farko.

Jagora ya kara da cewa “akwai bukatar marubutanmu su yi amfani da basirarsu wajen rubuce-rubucen littatfai masu ma’ana da yada ilimi da zai taimaki al’umma a addinisu da al’adunsu na kunya da kara da sanin ya kamata da kuma abin da ya shafi lafiya da bunkasar tattalin arziki da zaman lafiya,” kamar yadda ya bayyana wajen kaddamar da wannan littafi a ranar Lahadi da ta gabata.

Tunda farko a nasa jawabin, marubucin littafin Malam Hamisu Ibrahim ya ce ya rubuta littafi ne domin bada gudummawarsa a wannan fanni da kuma ya yaba wa iyaye da malamansa da sauran al’umma na karamar hukumar Dala da karamar Hukumar Nassarawa dama Kano baki daya musamman wadanda suka bada gudunmawa ta shawara dama dukkanin sauran taimako don samun nasarar fitowar wannan littafi da kaddamar da shi.