An samu aukuwar gobara a Kasuwar Panteka a Kaduna

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Da safiyar wanna Laraba aks samu aukuwar gobara a fitacciyar kasuwar nan ta Panteka da ke Kaduna.

Wani ganau mai suna Malam Isiyaku, ya ce gobara ta fara ne da misalin karfe na dare 12.

Ya kara da cewa, ya zuwa lokacin da aka nemi jin ta bakinsa ba a kai ga gano dalilin aukuwar gobarar ba.

MANHAJA ta tattaro cewa, gobarar ta kone shaguna masu yawa wanda hakan ya haifar da asarar dimbin dukiya.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi a jihar ba su ce uffan ban kan iftila’in gobarar.

Ga wani bangare na bidiyon gobarar:

By Editor