Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi shugabannin kananan hukumomin shida da laifin yajin aikin da malaman makarantun firamare ke cigaba da yi a yankin.
Wike, wanda ya yi wa ’yan jarida jawabi a ranar Talata a Abuja jim kadan kafin wani taron gaggawa da hukumomin tsaro, ya ce jami’an kananan hukumomin ba su cika aikin da aka dora musu ba.
A ranar Lahadin da ta gabata ne Kungiyar Malamai ta babban birnin tarayya Abuja ta umurci malaman firamare da su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 15 ga watan Janairu.
Yajin aikin dai an dara ne inda inda aka tsaya bayan na farko da kungiyar ta dakatar a shekarar 2023 kan rashin biyan kashi 40 cikin 100 na alawus da kuma karin albashi na watanni 25 da dai sauransu.
NUT ta dakatar da yajin aikin ne a ranar 2 ga Oktoba, 2023 don ba da damar warware matsalolin cikin makonni shida, amma ba a yi komai ba.
Don haka ministan ya dora alhakin yajin aikin da aka dade ana yi a kan shugabannin, sannan ya bukace su da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu.
