Rundunar ‘Yan Sandan Birnin Tarayya (FCT) ta tabbatar da cafke wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Chinaza Phillip, wanda ake zargin yana daya daga cikin batagarin da suka addabi yankin Abuja da sace-sacen mutane.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce sun kama wanda ake zargin ne a ranar Alhamis a Jihar Kaduna.
Ta kara da cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata aka mika wa rundunar Chinaza Phillip wanda a halin yanzu ake ci gaba da tsare shi.
Cikin sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce, “Rundunar ‘Yan Sandan FCT na sanar da cewa, jami’an ‘yansanda a jihar Kaduna sun damke wani Chinaza Phillip wanda ya gawurta a harkar garkuwa da mutane Abuja a ranar Alhamis, 18 ga Janairu, 2024.
“Kuma an mika wanda ake zargin ga Rundunar ‘Yansandan FCT a ranar Juma’a, 19 ga Janairu, 2024, wanda a yanzu haka ake ci gaba da tsare shi.”
A lokutan baya-bayan nan dai babban birnin na fama da matsalar tsaro inda ‘yan bindiga kan shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane.
