Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Legas ta doke Dubai, Barcelona, Miami inda ta zama birni na 19 mafi kyawun ziyarta a duniya.
Rahoton Time Out, wani kamfanin watsa labarai na Birtaniya ne ya bayyana hakan.
Time Out ya ce, an yanke wannan shawarar ne daga wani bincike na sama da birane 20,000 a fadin duniya.
A cikin rahoton da aka buga a ranar Talata, Time Out ya ce ya yi aiki tare da Potentia Insight, wani kamfanin bincike, don karfafa ingancin binciken.
Cape Town na Afirka ta Kudu, Legas na Nijeriya da Accra na Ghana ne kawai biranen Afirka da suka fito cikin jerin.
Brand Finance City Index a cikin 2023 ya sanya Legas a matsayin birni na biyar mafi kyau a Afirka da ke da sha’awar rayuwa, aiki, da saka hannun jari, a cewar wani rahoton.
Legas da Nairobi sun kasance a bayan Cape Town (Afirka ta Kudu), Alkahira (Masar), Johannesburg (Afirka ta Kudu), da Casablanca (Maroko).
Rahoton ya karfafa gwiwar ‘yan kasashen duniya da su ziyarci birnin.
Ga cikakken jerin birane mafi kyau a duniya;
- Birnin New York, Amurka
- Cape Town, Afirka ta Kudu
- Berlin, Jamus
- Landan, Birtaniya
- Madrid, Sifaniya
- Birnin Meziko, Meziko
- Liverpool, Birtaniya
- Tokyo, Japan
- Roma, Italiya
- Porto, Portugal
- Paris, Faransa
- Mumbai, Indiya
- Lisbon, Portugal
- Chicago, Amurka
- Manchester, Birtaniya
- Sao Paulo, Brazil
- Los Angeles, Amurka
- Amsterdam, Netherlands
- Legas, Nijeriya
- Melbourne, Ostiraliya
- Naples, Italiya
- Singapore
- Miami, Amurka
- Bangkok, Thailand
- Lima, Peru
- Budapest, Hungary
- Beijing, China
- Dubai, United Arab Emirates
- Montreal, Kanada
- Glasgow, Birtaniya
- Sydney, Ostiraliya
- Bueno Aires, Argentina
- Kuala Lumpur, Malaysia
- Manila, Philippines
- Seoul, Koriya ta Kudu
- Hanoi, Vietnam
- San Francisco, Amurika
- Barcelona, Spain
- Abu Dhabi, UAE
- New Orleans, Amurika
- Philadelphia, Amurika
- Austin, Amurika
- Boston, Amurka
- Accra, Ghana
- Marseille, Faransa
- Taipei, Taiwan
- Istanbul, Turkiyya
- Osaka, Japan
- Hong Kong, ChAna
- Vancouver, Kanada.
