*Shugaban yana aiki dare da rana don gyara Nijeriya, inji ministan labarai
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya roki ‘yan Nijeriya da su kara hakuri da Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa, ya yi wuri a yanke kauna ko a dawo daga raikiyar gwamnatin daga lokacin da ya dare gadon mulki zuwa yanzu.
Tun da ya hau kan karagar mulki a watan Mayu, Shugaba Tinubu ya bullo da wasu tsauraran sauye-sauye a fannin tattalin arziki, irin su shakewar Naira da kuma cire tallafin man fetur da ake ta cece-kuce a kai da nufin qarfafa arzikin kasa.
To, sai dai kuma sauye-sauyen sun haifar da tashin gwauron zabi a cikin tsadar rayuwa tare da hauhawar farashin kayayyaki.
Amma da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a jiya Alhamis, Idris ya bayyana fatan cewa, garambawul din zai samar da sakamakon da ake so nan gaba.
Ya ce, “Ina so ku tuna cewa, Shugaban Kasa ya cika wata bakwai a kan karagar mulki. Ba zan ba da uzuri ba cewa, watanni bakwai kadan ne kawai. Amma don shirin dogon lokaci, ku na bukatar karin lokaci mai yawa, domin sanya tsarin aiki. Amma ba shakka, yayin da ku ke tafiyar dakace, za a samu firgita, tashin hankali da tarwatsewar lokaci-lokaci waɗanda za ku samu.
“Amma tunanin shugaban kasa a fili ya ke: ya na so ya kai Nijeriya ga cigaban da ake bukata.
“Ya na aiki dare da rana, don cimma hakan. Kowacce rana, ministocin da kowa da kowa su na aiki a wannan hanya, amma har yanzu ba a ga sakamakon ba. Mu na rokon ’yan Nijeriya su kara hakuri.”
Yayin da ya amince da cewa, gwamnati na sane da irin wahalhalun da ’yan Nijeriya ke fuskanta, ministan ya tabbatar da cewa, shugabannin kasar na bakin kokarinsu wajen ganin an sauya yanayin.
A cewarsa, gwamnatin Tinubu, bayan cire tallafin, ta vullo da wasu matakai don dakile tasirin matakin.
Ya lissafta wasu daga cikinsu da suka haɗa da biyan qarin albashin na Naira 30,000 ga ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da shirin kaddamar da motoci masu amfani da gas na CNG a fadin kasar.
Binciken da Blueprint Manhaja ta yi ya nuna cewa, talakawan Nijeriya masu karamin karfi da matsakaita su na kuka kan yadda kayayyaki ke tashin gwauron zabo, musamman kayayyakin abinci da na masarufi da sauransu. Hatta masu karfi a kasar sun fara tsorata da yanayin yadda kayan ke faman tashi, musamman ma Dalar Amurka.
Sai dai kuma a jiya Gwamnatin Tarayya ta bai wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) umarnin fito da ajiyayyiyar Dala, don a samu Dalar ta karye a kasuwar shunku, wato kasuwar cikayya da hada-hadar kudi.
Masana na ganin cewa, daukar ire-ire waɗannan matakai zai iya kawo sauyi a nan gaba kadan.
