Ayyukan ‘yan daba sun tilasta wa INEC dakatar da zaɓen cike giɓi a Kano da sauransu

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da ci gaba da zabe a wasu mazabun da ake sake zabe a jihohin Kano da Enugu da Akwa Ibom saboda matsalolin da suka hada da sace jami’an zabe da sauransu.

Yankunan da dakatarwar ta shafa sun hada da Enugu ta Kudu 1, Mazabar Tarsyya ta Ikono/Ini a Akwa Ibom da kuma Mazabar Kunchi/Tsanyawa a jihar Kano.

Bayanin haka na kunshe ne cikin sanarwar da INEC dinnta fitar a ranar Asabar mai dauke da sa hannun Kwamishinanta na kasa kan shaa’nin yada labarai, Sam Olumekun.

Hukumar ta dauki wannan mataki bayan da ta bayyana tun fari cewa, tana bibiyar matsalolin da suka taso da suka hada da sace kayazan zabe da matasalar ‘yan daba da sauransu a jihohin da zaben ya shafa.

A cewa INEC, an dakatar da sake zabe a mazabar Kunchi/Tsanyawa a Jihar Kano inda aka dakatar da zaben a baki daya rumfunan zabe goman da ke yankin Karamar Hukumar Kunchi saboda ayyukan ‘yan daba.

Haka nan, ta ce an dakatar da zabe a baki daya rumfunan zabe guda takwas wanda aka samu babu asalin takardar sakamako don masu kada kuri’a su duba kafin fara zabe a mazabar Enugu ta Kudu 1.

Sai kuma Jihar Akwa Ibom inda INEC an dakatar da zabe a wasu rumfuna biyu, daya a yankin Ƙaramar Hukumar Ini gudan kuma a yankin Karamar Hukumar Ikono, inda ‘yan daba suka sace kayayyakin zaben kakaf.

Hukumar ta ce matakin da ta dauka ya yi daidai da Sashe na 24(3) na Dokar Zabe ta 2022.