Matsalar tsaro: Ƙabilun Nasarawa sun buƙaci a dakatar da sabuwar ƙungiyar ‘yan bangan Nomadi

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Wata haɗakar ƙungiyoyin shugabannin matasan ƙabilu daban-daban da ake kira da Furum of Ethnic Youth Presidents a Turance a Jihar Nasarawa, ta yi kira na musamman ga Gwamnatin Tarayya ta gaugauta dakatar da ayyukan ‘yan sabuwar ƙungiyar nan na ‘yan bangan Nomadi da aka ƙaddamar kwanan nan a jihar.

Shugaban haɗakar ƙungiyoyin, Silas Dauda Yilmi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar ‘yan jarida da ke Lafiya, babban birnin jihar.

Ya ce, kiran ya zama wajibi don kafa sabuwar ƙungiyar na ‘yan bangan Nomadi ɗin ba shakka na tattare da ayar tambaya.

Ƙungiyoyin ƙabilu na jihar sun ce sun yi mamaki matuƙa yadda shugaban al’ummar Fulani na ƙasa, Alhaji Bello Abdullahi Boɗejo ya yi alƙawarin kwashe sama da mutum 1,144 a cikin ‘yan bangan na Nomadi ɗin inda ya kuma yi alƙawarin magance matsalar tsaro a jihar a cikin makonni 6 kacal.

“Mun ƙi, ba za mu amince da wannan ƙungiyar nan na ‘yan bangan Nomadi ɗin ba tunda ba ƙabilu daban-daban ne dake jihar nan suka kafa ta ba don guje wa kada daga bisani a riƙa yin amfani da su a matsayin ‘yan ta’adda, shi ya sa muke Kira a gaugauta dakatar da ayyukansu a jihar nan da ma ƙasa baki ɗaya, musamman idan aka yi la’akari da ƙalubalen tsaro da jihar nan da ma ƙasa baki ɗaya ke fuskanta a yanzu,” inji shi.

Hauhawar Farashi: Dole gwamnoni su sauke nauyin da ke kansu – Fasua

AFCON: Tinubu ya janye aniyyarsa ta zuwa kallon wasan Nijeriya na ƙarshe, ya wakilta Shettima a madadinsa

Haɗakar ƙungiyoyin ta ƙara da cewa maimakon kafa ƙungiyar kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta samar wa duka fonnonin tsaron ƙasa da ingantaccen makamai da sauran kayayyakin aiki domin ba su damar tunkarar matsalolin tsaron yadda ya dace.

Idan za a iya tunawa, a ‘yan kwanakin nan ne dai ƙungiyar nan na Miyetti Allah Kautal Hore na ƙasa ta ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar na ‘yan bangan Nomadi din a jihar Nasarawa wadda ta ƙunshi kimanin matasan Fulani 1,144 tare da yin alƙawarin kafa ire-iren ‘yan bangan a duka sauran jihohin ƙasar nan 36 baki ɗaya ciki har da babban birnin tarayya, Abuja.

By Editor