Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya saka hannu kan dokar da za ta hana mutane ɓoye kayan abinci.
Kafa wannan doka na nufin hana wasu ‘yan kasuwa da ake zargi da ɓoye kayan abinci a rumbuna daban-daban don kayan abincin su yi tsada.
Kazalika, Gwamnan ya kafa wani kwamiti na musamman da za a ɗora wa alhakin bi lungu da saƙo na jihar don zaƙulo mutanen da suke ɓoye kayan abinci.
Dokar ta kuma haramta duk wani yunƙuri na ɓoye kayan abinci a duk faɗin jihar.
Haka nan, dokar ta lissafta kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, masara, gero, dawa, waken suya, gyaɗa da ma duk wani nau’in kayan abincin da ƙarancinsa zai jefa al’ummar jihar Katsina cikin halin ha’ula’i.
Dokar ta kuma bayyana cewa, duk wani mutum ko kamfanin da aka samu da laifin ɓoye kayan masarufi, to ya saɓa dokar da za a iya hukunta shi ƙarƙashin sashe na 114 na kundin penal code.
Sannan hatta wurin da aka kama cewa ana ɓoye waɗannan kayan abinci, za a ɓarke shi a fitar da abincin don sayar wa al’umma a farashin da ya dace.
Ta ɓangaren kwamitin kar-ta-kwana na task force da Gwamnan ya kafa kan wannan batu kuwa, an ɗora masa alhakin zaƙulo masu ɓoye kayan masarufin a cikin jihar.
Akwai kwamiti da ya haɗa da jami’an tsaro waɗanda za su kamo tare da gurfanar da waɗanda aka samu da laifin, kwamitin zai kuma gana da masu ruwa da tsaki kan harkar kayan masarufi a jihar don gudun kitso da kwarkwata.
Bayan haka, kwamitin zai riƙa kula da yadda ake safarar kayan abincin, daga sassan jihar daban daban da ma tsallakawa da shi ƙasashen waje.
Ana kyautata zaton kwamitin zai ƙunshi shugaba da ƙarin mambobi 10 da za su gudanar da wannan aiki kamar yadda mai taimakawa gwamnan a kafafen yaɗa labarai na zamani Isah Miƙdad ya bayyana wa Manhaja.
