Daga BASHIR ISAH
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas ya rage ranakun aiki wa ma’aikatan jihar zuwa uku maimakon biyar da aka saba.
A sanarwar da ya bayar a ranar Alhamis, Sanwo-Olu ya ce daga yanzu ma’aikatan gwamnatin jihar da ke mataki na 1 zuwa 14 sau uku kacal za su riƙa tafiya aiki a mako.
Ya ce ya gwamnatinsa ta ɗauki wannan mataki ne domin sauƙaƙe wa ma’aikatan jihar ƙuncin tattalin arzikin da ake fuskanta.
Ya bayyana haka ne a jawabin kai-tsaye da ya yi wa ‘yan jihar a ranar Alhamis domin sanyaya musu rai dangane da tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasa.
Sai dai Gwmnan ya ce ma’aikatan fannin kiwon lafiya za su ci gaba da tafiya aiki kwana biyar a mako kamar yadda aka saba, amma cewa gwamnati za ta samar musu da ƙarin motocin da za su riƙa jigilarsu zuwa wajen aiki.
Kazalika, ya sanar da zabtare kashi 25 na kuɗin motocin gwamnatin da ke jigilar al’umma a faɗin jihar.
