Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kwastom ta ziyarci tashar iyakar Nijeriya da jamhuriyar Nijar bayan ɗage takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar.
Hukumar ta ce ɗage takunkumin da kuma maido da wutar lantarki shi ne dalilan ziyarar tare shirya komai na sake buɗe iyakar Illela.
Kazalika ta buƙaci mazauna yankin da masu ruwa da tsaki na al’ummar yankin kan iyakar Illela da ke Sakkwato da su bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa gabanin sake buɗe iyakar da jamhuriyar Nijar.
Kamal Muhammad, Kwanturolan NCS mai kula da yankin Sakkwato/Zamfara, a ranar Talata, ya ziyarci iyakar Illela.
Muhammad ya ce matakin da ƙungiyar ECOWAS ta ɗauka na ɗage takunkumin da aka ƙaƙabawa Jamhuriyar Nijar na iya haifar da sake buɗe iyakokin ƙasar.
Kwanturolan ya ce sun kai ziyarar duba halin da ake ciki da kuma yin mu’amala da ‘yan kasuwa da mazauna yankin.
“Ziyara ta tashar kan iyakar Illela ita ce in tabbatar da cewa an shirya komai don sa ranar da za a sake buɗe iyakar,” in ji shi.
“Ɗage takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa jamhuriyar Nijar da kuma maido da wutar lantarki a maƙwabciyarta, shi ne dalilan ziyarar domin ganin an shirya komai na sake buɗe iyakar Illela yayin da muke jiran umarni na ƙarshe.”
Ya gargaɗi mazauna al’umma kan fasa-ƙwaurin da a cewarsa ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki.
A watan Yulin shekarar 2023, Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ƙaƙaba wa jamhuriyar Nijar wasu takunkumi bayan da shugabannin sojoji suka tsige Mohamed Bazoum, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bisa tafarkin dimokuraɗiyya.
A wani ɓangare na takunkumin, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sanar da rufe iyakokinta na ƙasa da na sama da Jamhuriyar Nijar.
A baya-bayan nan ƙungiyar ECOWAS ta ɗage wasu takunkuman da ta ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso, da kuma Mali.
