Kada ku ƙyamaci masu roƙon ku taimaka musu

Spread the love

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Halin ƙuncin rayuwa da yunwa da ake fama da shi a wannan lokaci na koma bayan tattalin arziki da talauci a ƙasa, ya jefa iyalai da magidanta da dama cikin wani mawuyacin rayuwa. Samun damar cin abinci sau uku ko sau biyu a wuni ya fara zama tarihi a wajen wasu.

Magidanta da dama sun zama maroƙan ƙarfi da yaji, tun mutum na jin nauyin ya yi roƙo, har ya fara zama masa jiki, don dai neman abin da zai ciyar da iyali, ko da kuwa shi zai haƙura ya kwana da yunwa.

Muna sane da cewa, babu wani ɗan Nijeriya da wannan tsananin bai tava ba, sai dai tsiraru waɗanda Allah ya tarfawa garinsu nono! Hatta masu arziki da rufin asiri da muke musu kallon su ne dama-dama to, su ma yanzu kuka suke yi.

Koda ba don sun rasa gabaɗaya ba, don irin yadda nauyin ’yan’uwa da abokan da aka taso tare ke ƙara hawa kansu. Sannan abin da aka saba samu a baya yanzu ya fara raguwa ba kamar da ba.

Abin tausayi ne yadda za ka ga mutumin da a baya yake da rufin asiri, amma yanzu talauci ya sarƙafe shi, da qyar ake samun abin da za a ci a gidansa. Idan kana son ka ga zahirin hakan kai ziyara gidan wani abokinka ƙaramin ma’aikaci, ko ɗan kasuwa mai ƙaramin jari, ko wanda ke ci a ƙarƙashin wani da shi ma harkokinsa suka fara ja da baya.

Ko kuma ka leƙa maƙwafta irin gidajen da maigidan ke kwance yana fama da jinya ba ya iya fita aiki ko kasuwa, kuma masu ɗan tallafa musu sun fara gajiya, ga akasarin yaransa ƙanana ne. Ko iyalin da maigidan ya rasu ya bar yara marayu da mata biyu ko uku suna zaune babu tabbas ɗin samun abin da za su ci yau ko gobe.

Irin waɗannan mutane idan ka gansu a titi sun fito suna roqo, ko suna bibiyar ’yan uwa da abokan arziki, don a tallafa musu da abin da za su ci, bai kamata a tsangwame su ko kyare su ba. Ko ba ka da abin da za ka bai wa mutum kada ka wulaƙanta shi ko ka muzanta shi don ya roƙi abin da zai ci.

Ba kowa ne ke jin daɗin roƙo ba, kuma ba kowa ne ya zama ɗan maula ko ɗan kala kamar yadda wasu ke faɗa ba. Alƙur’ani mai girma ya faɗa mana cewa, kada ku kyari masu zuwa roƙonku!

Kodayake ana samun wasu baragurbin mutane da suka mayar da roƙo ya zama sana’arsu, ba sa aikin komai sai dai bibiyar abokai da maƙwafta ko masu hali suna roƙonsu basu kuɗi, don biyan wata buƙata da ta takura su, musamman a kafafen sada zumunta ko ta waya. Amma hakan ba dalili ne da zai sa duk wani magidanci ko mai ƙaramin ƙarfi da ya zo maka da buƙata ya zama cima-zaune ba.

Ko da kuwa a baya ka san shi a matsayin mutum mai rufin asiri, ba abin mamaki ba ne a yanzu ya samu kansa cikin jarabawar rayuwa, ko karayar tattalin arziki, wanda yana iya faruwa da kowa. Idan ka ga ya samu kansa cikin masu roqon abin da za su ci kada ka ƙyamace shi, ko ka sa shi a gaba kana gulmarsa da aibata shi a cikin mutane. Gobe kai ma Allah yana iya jarabtarka, kuma ya zama shi ne ke da damar taimaka maka.

Duk da kasancewar addinin Musulunci da mutuntaka ta ɗan Adam ba su lamuncewa mutane su zama maroƙa ba, amma roƙo na iya zama dole ne a yanayin da mutane suka rasa madafa ko aka shiga cikin annoba da ƙangin yanayin da ya shafi kowa. Don haka ya kamata a riƙa yi wa mutane uzuri, a halin da ake ciki, kada a aibata su ana nuna basu da juriyar babu, ko basu da tawakkali da sauransu.

Yunwa fa bata san wannan ba, duk dauriyar mutum akwai inda yake da rauni, kuma raunin wani ba illa ba ce, lalura ce! Babu ma kamar idan batun iyali ya gifta, don kuwa duk wani magidanci nagari da ya san inda ke masa ciwo, ba zai tava kwantar da hankalinsa ba, idan iyalinsa na zaune cikin yunwa da ƙuncin rayuwa.

A irin wannan yanayin ne da ake hantarar masu roƙon abin da za su ciyar da iyalinsu, ake samun wasu masu raunin suna aikata wasu abubuwa da basu kamata ba, kamar irin su sata da bin maza, waɗanda ba za su bai wa mace taimako ba, sai in za ta ba da kanta gare su.

Wasu vata-gari na amfani da wannan yanayin da ake ciki suna ɓata ‘ya’yan mutane da matan wasu, don ganin halin da suke ciki, suna yi musu tayin samun taimako daga garesu idan su ma za su amince su taimaka musu, wato su yarda a yi fasiƙanci da su. Wa’iyazubillahi!!

A irin wannan lokaci ne, ake samun ƙaruwar mace-macen magidanta, sakamakon lalurori masu nasaba da hawan jini da bugun zuciya, saboda yawan tunani, tsoro, da firgici kan halin da su da iyalinsu ke ciki. Mutane da dama masu kyan sura da kwarjini sun lalace sun fita hayyacinsu, saboda yunwa da ƙuncin rayuwa da suka samu kansu a ciki. Wasu tun tasowarsu basu tava ganin jarabawar rayuwa irin wannan da ake ciki a yanzu ba.

Kwanaki na ga wani labari da ake yaɗawa a zaurukan sada zumunta da ke nuna cewa wata mata a Jihar Kaduna ta dafa ruwan zafi ta sa gishiri a ciki ta bai wa yaranta, saboda da rashin abin da za ta ba su su ci.

A dalilin haka kuma suka rasa ransu, har hakan ya haifar da zanga-zangar mata a cikin garin saboda nuna damuwa da halin da ake ciki. Labarin mutanen da ke rataye kansu su mutu, don rasa mafita a rayuwarsu, ya daina zama abin mamaki, sakamakon yadda ya fara zama ruwan dare.

Har zuwa yaushe za a cigaba da irin wannan rayuwa? Muna samun labarin yadda ’yan siyasa da jami’an gwamnati ke cewa suna iyaka ƙoƙarinsu don shawo kan lamarin, da yadda ake cewa gwamnati za ta buɗe iyakokin ƙasa don shigo da wasu nau’ikan kayan masarufi, don rage raɗaɗin da talakawa ke ciki.

Amma shin hakan ya wadatar kuwa? Lallai akwai buƙatar gwamnati ta fitar da wasu sabbin dabaru da tsare-tsare da za su kawo sauyi na musamman a rayuwar ’yan ƙasa. Don gaskiya ana ji a jiki, jama’a na wahala sosai.

Sannan kamar yadda muka saba faɗa a wannan shafi, ba zai yiwu jama’a su cigaba da naɗe hannu suna jiran taimako daga gwamnati ko wasu ’yan siyasa, su shiga neman qarin hanyoyi da dabarun neman sana’o’i da abin dogaro da kai. A irin wannan lokaci ne ake neman sana’a goma, da ake ce maganin mai gasa, domin idan ba a dace a nan ba za a dace a can, kuma a riƙa haƙuri da ƙaramar riba.

Sannan a ɓangaren iyali a riƙa taimakawa juna ana tallafawa da abin da ba zai gagara ba, don a rufawa kai asiri. A rage ɗora wa kai nauyin da bai zama tilas ba, kuma a koyi kawar da kai daga wasu abubuwan da ke faruwa a dalilin rashi ko talauci, savanin yadda aka saba gani a baya. Ba lallai ne nishaɗi da jin daɗin da ake samu a shekarun baya su ɗore ba, har sai abubuwa sun daidaita.

Malamai da sauran ’yan ƙasa su ƙara himmatuwa da addu’o’i da azumi don neman taimakon ubangiji, da samun sassauci a halin da ake ciki. Mu riƙa taimakawa marayu da masu ƙaramin ƙarfi da ke tare da mu, idan Allah Ya hore mana. Kada mu riƙa hantarar marasa shi, ko tsangwamar masu roƙon mu taimaka musu. Mu rufawa kai asiri, mu tallafawa juna, mu kuma nemi taimakon ubangiji kan duk abubuwan da ke faruwa da rayuwarmu!

By Editor