Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kula da Ɗanyen Mai da ake Fitarwa Waje (NUPRC), ta bayyana cewa an fara bayar da lasisin mallakar rijiyoyin mai na shekarar 2024.
Shugaban Hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe ne ya bayyana haka a Miami, Florida a ƙasar Amurika inda hukumar ta ɗauki nauyin wani nune-nune, tare da haxin-gwiwar Ƙungiyar Masu Fasahar Harkokin Ɗanyen Mai ta Nijeriya (PETAN).
Hukumar ta ce rabon lasisin mallakar rijiyoyin ɗanyen mai a 2024 zai shafe tsawon watanni 9.
Yayin da Komolafe ya bayyana tandar nema da cancantar mallakar, ya ce tun a ranar 29 ga Afrilu aka yi sanarwar, wadda ya ce ta na da tasiri sosai wajen ƙoƙarin da ake yi na ganin an karkata ga bunƙasa kayayyaki masu amfani gas.
Ya ce akwai rijiyoyi 12 da za a bijiro da su a sassa daban-daban, kama daga kan tudu har zuwa na cikin teku.
“An zaɓi kowace rijiya domin tasirin da za ta samar wajen ƙara yawan kuɗaɗen asusun mu na ƙasashen waje da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
“A madadin Gwamnatin Tarayya, NUPRC za ta tantance dukkan waɗanda suka cancanci mallakar rijiyoyin bisa gasar cancantar tandar da za a buga. Za mu yi haka ne domin tabbatar da yin adalci ga masu zuba jari na cikin gida da na nan ƙasashen waje.”
Ya ce za su yi komai su baje shi a faifai bisa bin ƙa’idar Dokar Fetur ta 2021.
Rijiyoyin ɗanyen mai 12 da za a yi watanda:
Akwai manyan rijiyoyin mai masu faɗi sosai na ɗanyen mai, masu lamba: PPL 300-CS; PPL 301-CS, PPL 3008, PPL 3009, PPL 2001, PPL 2002, PPL 51, PPL 267, PPL 268, PPL 269, PPL 270 da PPL 271,” inji Komolafe.
