Daga MAHDI M. MUHAMAMAD
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin hamshaƙin ɗan kasuwa, shugaban rukunin kamfanonin Dantata, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a fadar shugaban aasa da ke Abuja a ranar Talata.
Lokaci na ƙarshe da aka ga mutanen biyu tare a bainar jama’a shi ne a shirye-shiryen zaɓen 2023, Tinubu ya ziyarci fitaccen ɗan kasuwan a Kano.
Ba a bayyana cikakkun bayanai kan tattaunawar ta ranar Talata ga jama’a ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
