Thomas Fuller: Masanin lissafi mafi sauri ɗan Afirika

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Thomas Fuller, wanda ake yi wa laƙabi da “Mai lissafin tunani”, ɗan asalin Afirka ne da masu satar bayi suka sace shi tun yana da shekaru goma sha huɗu, sannan suka sayarwa Turawa masu sayen bayi a shekarar 1724.

Fuller yana da tsananin fikira wajen warware matsalolin lissafi da ka, kuma a cikin ƙanƙanin lokaci.

Wata rana an tambaye shi, “daƙiƙu nawa ne a cikin shekara ɗaya da rabi” cikin minti biyu ya bada amsar cewa, “daƙiƙa miliyan arba’in da bakwai, da dubu ɗari uku da huɗu”.

Haka an taɓa tambayarsa; daƙiƙa nawa mutumin da ya shekara saba’in (70) da kwana sha bakwai (17) da awa sha biyu (12) “a cikin minti ɗaya da rabi yabada amsa cewa, mutumin ya rayu na daƙiƙu biliyan biyu, da miliyan ɗari biyu da goma, da dubu ɗari biyar da ɗari takwas (2,210,500,800).

Wani Bature da ke lissafa wa a takarda sai ya ce amsar da Fuller ya bayar akwai kuskure saboda anashi lissafin yawan daƙiƙun sun saɓa dana Fullar. Nan take Fulla ya ce masa shi ne ya yi kuskure a lissafin saboda bai lissafa da ‘shekara cif ba’. Nan take Baturen ya gyara lissafinsa sai amsa ta yi daidai da ta Fullar.

Ranar 29 ga Disamba, 1790, ita ce ranar mutuwar shahararren masanin lissafi Thomas Fuller, wanda aka sani da “Mai lissafin tunani”.

Ya mutu a ranar 29 ga Disamba, 1790, Marigayi Thomas Fuller bawa ne ɗan Afirka wanda aka sani da kwarewar ilimin lissafi. An kama shi a Afirka ta hannun turawan yamma masu sahen bayi, kuma aka tura shi zuwa Amurka a cikin shekarar 1724 lokacin yana ɗan shekara 14 kawai a duniya.

Ya kware a fannin lissafi, yana iya yin lissafin da ba a misaltawa. Wata rana da suka tambaye shi daƙiƙa (second) nawa ne a cikin shekara daya da rabi, sai ya amsa tambayar a cikin mintuna biyu kacal, daƙiƙa 47304000.

Masu goyon bayan kawar da kai da farar fata sun yi amfani da basirar sa a matsayin hujjar cewa baƙar fata sun yi daidai da turawa a hankali.

Thomas Fuller, babban masanin lissafi ne, amma kash an manta da tarihi.

Ranar 29 ga watan Disamba, 2024 ne yake cika shekaru 233 da rasuwa.

By ukarofi