
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙananan jami’an hukumar gidajen yari ta NCS, sun koka kan yadda ta gagara raba musu sabon kayan sa wa na hukumar a kyauta bayan bai wa manyan jami’anta.
Jami’an sun ce abun da ya ƙara dagula lamarin shi ne yadda hukumar ta sanya mallakar sabon kayan a matsayin ɗaya daga cikin rukunan jararbawar ƙarin girma da ta yi, wanda za’a gudanar daga ranar 1 zuwa 6 ga watan Yuli, 2024.
Wani jami’i da bai yadda a faɗi sunansa ba, ya ce a ayyukan da ake sanya inifom, a kan bai wa manyan jami’ai kyauta, amma ƙananan jami’ai, sai dai su mallaka da kansu.
Ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, ya fada wa jaridar ‘News Point Nigeria’ cewa an sauya kayan jami’an tun a shekarar 2019, inda ake ta ƙoƙarin gushewar tsohon, sannan an bai wa manyan jami’ai har zuwa matakin sufuritanda a kyauta, sai aka daina bayar wa, bayan doka ta hukunta a bai wa dukkan jami’ai inifom a kyauta matuƙar aka samu sauyi.
