Ana amfani da jirage masu zaman kansu wajen jidon kuɗin sata, inji Ministan Sufurin Sama

Spread the love

Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo, yace aña amfani da jirage masu zaman kansu wajen jidon kuɗaɗe da aka sata da safarar miyagun ƙwayoyi.

Ministan ya bayyana haka ne a yayin wani taro na hukumar sufurin jiragen sama, inda ya bayyana cewa taron ana yin sa ne domin kawo ƙarshe ayyukan bijirewa doka da jirage masu zaman kansu suke yi.

Keyamo ya ƙara da cewa, wasu dayawa sun karya ƙa’idojin lasisin da aka basu domin suyi aiki. Wanda hakan ya jawo ma Najeriya asarar kuɗaɗen shiga da dama.

Daga ƙarshe ya kafa kwamiti wanda zasu bincika ayyukan jiragen masu zaman kansu wanda Ado Sanusi ke jagoranta. Ya basu wa’adin watanni uku su kawo rahoton binciken nasu.

By ukarofi