
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙasashen Saudiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sun sanar da rage adadin lokacin gudanar da huɗubobin sallar jumma’a a masallatai saboda tsananin zafin rana da su ke fama da shi.
Al’ummar musulmi a ƙasashe da dama na duniya kan gabatar da sallar jumma’a ne da rana wacce masallata ke zama domin sauraron ta ciki da wajen masallaci da wuraren da babun rumfuna, don haka ƙasashen biyu suka yanke hukuncin hakan domin sauƙaƙa mu su kamar yadda addinin Musulunci ya karantar.
Shugaban ma’aikatar kula da harkokin addini na ƙasar Saudiyya ya ce, sun rage adadin lokacin huɗubar zuwa minti goma sha biyar a masallatan Ka’aba dake Makka da kuma na Manzon Allah (SAW) dake Madina saboda masallatan da ke sallah a wuraren da babu inuwa.
A ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kuwa, zafin rana ya haura digiri hamsin, don haka hukumomi suka umarci limamai da su riƙa yin huɗubar a mintuna goma har zuwa ƙarshen watan Oktoban shekarar nan domin kiyaye lafiyar masallata.
A ƙalla, mahajjata sama da 1,300 suka mutu a yayin gudanar da aikin hajjin shekarar nan sakamakon tsananin zafi.
