Ilimi da wayewar mutanen Bichi ya sa siyasa ba ta raba kansu – Kado

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

An bayyana cewa duk da bambance-bambancen siyasa na jam’iyyu daban-daban a ƙaramar hukumar Bichi, amma hakan bai hanasu zaman lafiya ba.

Shugaban Riƙo na Ƙaramar Hukumar Bichi, Hon Ahmad Kado Bichi shi ne ya bayyana haka cikin makon nan.

Ya ce al’ummar Bichi suna zaune lafiya da junansu kuma duk abinda za a yi ko bukukuwan sallar nan da aka yi ya sa babu wata matsala komai lafiya a ke zaune, don haka ya ce yana ganin cewa mutanen Bichi shugabanni da mabiya sun cancanci a yaba musu wajen haɗin kai da suke samu daga garesu kuma wannan abin farin ciki ne kuma a cewarsa wannan ya faru ne sakamakon yadda shugabanni a ƙaramar hukumar Bichi suka fahimci junansu kuma suke tafi da al’amuransu cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna kasancewar dama mutanen Bichi mutane ne masu ilimi da gogewa da wayewa, inji shi.

Haka kuma ya ce sakamakon zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Bichi yanzu haka da zuwansa a matsayin Kantoma a Bichi an yi ayyuka da dama a ci gaban al”umma kamar samar da tsaftatacen ruwan sha a wurare daban-daban ta hanyar gina rijiyoyin burtsatse da kuma hanyoyi na samar da ruwa da aka saba da su sai kuma inganta harkar lafiya ta hanyar gyara asibiti kamar asibitin ƙauyen Yola da ke mazaɓar Badume ga kuma gine-ginen kwalbati da dama da ƙaramar hukumar ta aiwatar a ƙarƙashin shugabancina na riƙo to kuma wannan nasara ta samu ne ta hanyar sahalewar gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, da kuma mataimakinsa Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo, kwamishinan kula da ƙananan hukumomi da masarautu na Jihar Kano

By ukarofi