Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, ta gudanar da bikin cika shekaru 30 da fara fitowar tawagar Nijeriya a gasar kofin duniya a shekarar 1994, lokacin da tawagar Super Eagles ta razana takwararsu ta ƙasar bulgaria wacce ake hangowa nasara inda suka fara gasar da ƙafar dama.
Tawagar ta Super Eagles ta fara bayyana a gasar kofin duniya a shekarar 1994, inda ta kara da takwararta ta Bulgaria wacce ke cike da ‘yan wasa masu ƙwazo.
Duk da cewa an bai wa Nijeriya matsayin da ya ɗara na takwarorinta na Turai, duk da haka ana yi musu kallon raini har sai da ta lallasa ƙasar Bulgaria da ci 3 da nema, a zamanin.
Ƙwallon Rashidi Yekini, wanda ya fara ci wa Nijeriya ƙwallon farko a gasar kofin duniya da waɗanda Daniel Amokachi da Emmanuel Amunike suka ci sun wadaci Super Eagles samun galaba akan Bulgaria, inda ta shelanta shigowarta fagen gasar ta duniya.
FIFA ta tuna fara shigowar Nijeriya gasar a shafinta na x, fifa ta jinjinawa bajintar tawagar super eagles a gasar cin kofin duniya na shekarar 1994, ta hanyar wallafa hotunan ƙwallon da Rashidi Yekini da tawagar Nijeriyar suka ci, da taken; “Shekaru 30 A Yau: Super Eagles Ta Samu Nasararta Ta Farko A Gasar Kofin Duniya.
Bayan samun galaba akan Bulgaria, Nijeriya ta yi rashin nasara a hannun Argentina kafin daga bisani ta doke ƙasar Greece domin samun gurbi a rukuni na gaba na gasar.
Rashin nasara da ci 2 da 1 a hannun Italiya a rukunin ‘yan 16 Nijeriya na nufin kawo ƙarshen fafatawarta a gasar a matakin rukuni, saidai har yanzu bajintar da ta nuna a fitowarta ta farko na zuciyar magoya bayan wasan ƙwallon ƙafa.
