Bagudu ya jinjina wa ƙoƙarin hukumar finafinai ta Nijeriya

Spread the love

 Daga AISHA ASAS 

Mai Girma Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare- tsare, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da masu ruwa da tsaki da harkar finafinan Najeriya su tallafa wa domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da Babban Daraktan hukumar, Dakta Ali Nuhu da manyan jami’an hukumar suka kai masa ziyarar aiki a ma’aikatar a Abuja.

Abubakar Bagudu ya yi nuni da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa ma’aikatar al’adu da ƙirƙira da masaniyar zamanta ɗaya daga cikin ma’aikatun da ke samarwa ƙasa kuɗin shiga da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

A cewar ministan, “Babbar ƙadararmu ita ce masana’antar ƙere-ƙare, kasancewar ta a sahun gaba wurin samar da aikin yi.”

Don haka ya yi kira ga Darakta Janar na Hukumar NFC da ya samar wa matasa damammaki masu ma’ana don cin gajiyar sana’ar.

Bagudu ya kuma shawarci hukumar da ta nemi haɗin gwiwa da KOICA na Koriya ta Kudu, Japan da kuma ofishin jakadancin Faransa, don ciyar da masana’antar ƙere-ƙare na ƙasar gaba.

Ministan ya bayyana Ali Nuhu, a matsayin wani jigo a gwamnati da zai iya yin amfani da ƙwarewarsa wajen isar da saƙwanni masu inganci na ƙarfafa gwiwa ga yan Nijeriya da ke fafutukar ganin sun samu ingantacciyar rayuwa.

Da yake nasa jawabin, Darakta Janar na NFC, ya ce maƙasudin ƙara girman kasafin kuɗin hukumar shi ne, samun damar cimma ayyukan da aka sanya a gaba. Ya kuma yi nuni da cewa, ƙarin kasafin kuɗin zai bai wa hukumar damar kula da ofisoshin hulɗa da jama’a, da inganta wurin zama na dindindin, da inganta ma’aikatan da ake da su da kuma ɗauke ma’aikatan da suka tsufa.

A cikin jawabin maraba, Darakta Misis Elizabeth Egharevba ta ce “Masana’antar nishaɗantarwa na da gudunmawa da za ta iya bayarwa ga ci gaban tattalin arzikinmu kuma muna da tabbacin naɗa ku da shugaban ƙasa ya yi, za ku sami ƙarin nasara.”

By ukarofi