Tsohon mijin Diezani ya roƙi kotu ta hana ta amfani da sunansa

Spread the love

Tsohon mijin tsohuwar ministan man fetur ta ƙasa, Diezani, ya shigar da ƙara kotu kan hana ta amfani da sunanshi bayan mutuwar auren su.

Ya roƙi kotun ta umarci Diezani ta dawo da tsohon sunanta na Agama kafin suyi aure. Ya umarce ta sanya sanar da wannan sunan a jaridun Najeriya da Ingila.

Ƙarar an shigar da ita ga babbar kotun Jihar Legas da ta daina amfani da sunan shi. Saboda yin haka na masa barazana sosai ga kasuwancin shi da mutuncin shi.

By ukarofi