Yan Najeriya na cece kuce akan ƙona makaman biliyan goma da hukumar kwastom za tayi.
Hukumar kwastom a yayin wani atisayen su, sun kama kwantena cike da bindigogi 844, da harsashai 112,500 a birnin fatakwal.
Makaman an ɓoye su a cikin kayan katako irin su kofa, jakukuna, da kayan karfe. Kwantenar da aka kama, ta taso ne daga ƙasar turkiya, wanda harajin da aka biya mata ya kai adadin biliyan huɗu.
Amma daga ciki cece kuce da ake wani ya bayyana a shafin sa na X cewa “kuna son ƙona makamai na biliyan huɗu bayan sojoji na kukan basu da makamai isassu?”
