Sarkin Katsina ya jagoranci sallar roƙon ruwa

Spread the love

Daga SANI NURA da BELLO ABUBAKAR BABAJI

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya jagoranci dandazon mutane sallar roƙon ruwa a jihar Katsina.

An gudanar da sallar ne a safiyar ranar Alhamis a filin Idi biyo bayan shafe kwanaki 16 da aka yi ba a yi ruwa ba.

Limamin babban masallacin Katsina, Imam Gambo Mustapha shi ya yi limancin sallar inda al’umma ta yi kira ga sauran ƴan jihar da su yi irin ta a sassa daban-daban na faɗin Jihar.

Masallatan sun ce an yi hakan ne ganin yadda amfanin gona ke bushewa tare da fuskantar barazanar lalacewa saboda ɗaukar sama da mako biyu da ba a samu ruwan sama ba.

Ɗaya daga cikin masallatan, ya yi kira ga al’umma da su guji saɓa wa Allah a cikin al’amura su na yau da kullum, sannan kuma shuwagabanni su ma haka, domin a halin yanzu kayan abinci ya yi tsada ta yadda al’umma na cikin mawuyacin hali.

By Babaji