Da ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta hana lauyoyi hira da ‘Yan jarida kan rikicin Masarautar Kano

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata babbar kotun Jiha a Kano ta fitar da umarni da ke hana lauyoyi amsa tambayoyin Ƴan jarida kan rikicin Masarautar Kano.

Mai Shari’a, Amina Adamu Aliyu ce ta faɗi haka a yayin wani zaman kotu da ta jagoranta kan batun a ranar Alhamis.

A ranar 25 ga watan Mayu, 2024 ne Antoni Janar na Kano da Kakakn majalisar jihar da kuma majalisar dokokin Jihar suka shigar da wata takarda da ke ƙunshe da ƙwance rawanin Sarki Aminu Ado Bayero da sarakunan Bichi, Rano, Gaya da kuma na Ƙaraye Kano.

Mai Shari’ar, ta ce umarnin zai yi aiki ne har zuwa lokacin da za a yi hukunci ƙarshen kan dambaruwar Masarautar.

A ƴan makonni da suka gabata ne gwamnatin Jihar ƙarƙashin jagoranci Abba Kabir Yusuf, ta fitar da sanarwar warware rawanin Sarki Aminu Ado Bayero da kuma ɗaura Sunusi Lamido Sunusi a matsayin sabon Sarkin Kano inda a ke ta rikici da ɓangaren da aka sauke kan ƙin amincewa da hukuncin gwamnatin.

By Babaji