Sanata Marafa zai janye tsayawar da yi wa Sanata Yari a EFCC

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sanata Kabiru Garba Marafa, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, ya bayyana aniyarsa ta janye tsayar da ya yi wa tsohon Gwamna Abdulaziz Yari.

Wannan matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara kunno kai a cikin jam’iyyar APC ta Zamfara, wanda ke nuna gagarumin sauyi a fagen siyasar jihar.

A baya dai, Sanata Marafa, ya taka rawa wajen ganin an saki Yari daga hannun Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa ta EFCC bisa beli. Ana kallon wannan aiki a matsayin wata alama ta sulhu, bayan shekaru da dama da aka shafe ana hamayyar siyasa. Marafa da Yari dai sun yi tashe-tashen hankula a tarihi, wanda ya nuna an gwabza ƙazamin faɗa a shekarar 2019, lokacin da Marafa tare da sauran ‘yan takarar gwamna suka haɗa kai ƙarƙashin ƙungiyar G8, inda suka nuna adawa da matakin da Yari ya ɗauka na naɗa Mukhtar Koguna a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara na APC.

A shekarar 2021, Marafa da Yari sun ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu, suka yi sulhu a bainar jama’a, tare da yin alƙawarin sabuwar tafiya ta aminci da haɗin gwiwa. Duk da haka, wannan sulhu bai daɗe ba. Daga baya Marafa ya zargi Yari da cin amana, musamman a lokacin zaɓen 2023, wanda ya haifar da sake ɓarkewar rikici tsakanin mutanen biyu.

Rikicin da ake fama da shi a cikin jam’iyyar APC ta Zamfara ya ƙara ta’azzara wannan rikici. Matakin da Marafa ya ɗauka na tsame kansa a harkokin Yari tare da janye wanda zai tsaya masa a EFCC ya nuna zurfin rigimar da ke tsakaninsu.

Wannan yunƙuri na iya haifar da gagarumin tasiri, ba wai ga ɗaiɗaikun mutanen da abin ya shafa ba, har ma da haɗin kan jam’iyyar da kuma fatan da za a samu a zaɓe mai zuwa.

Wani abin sha’awa, a cikin wacannan rigingimun cikin gida, jam’iyyar APC ta shirya wani shiri a ranar Asabar da ta gabata, da nufin haɗa kan dukkan ɓangarorin jam’iyyar domin fuskantar babban ƙalubale ga gwamnatin PDP mai ci a jihar Zamfara a zaɓen 2027. Wannan yunƙuri ya haifar da wata muhimmiyar tambaya: Shin Marafa zai yarda ya rungumi wannan sabon yunƙuri na sulhu da haɗin kan jam’iyyar?

Hanyar zuwa 2027 na cike da rashin tabbas ga APC ta Zamfara. Yayin da Marafa da Yari ke ci gaba da fafutuka a siyasance, dole ne jam’iyyar ta bi wannan hanya mai cike da gargada a tsanake domin ba da haɗin kai.

Watanni masu zuwa za su bayyana ko APC za ta iya magance rarrabuwar kawuna a cikinta, ta kuma yi taro tare domin cimma burin kwato mulki a Jihar Zamfara.

By ukarofi