
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A ranar juma’a, 5 ga Yuli, 2024 ne aka ɗaura auren tsohuwar tauraruwar Kannywood, Sadiya Gyale da angonta mai suna Mustafa Umar Kawu bayan sallar juma’a, a masallacin sharaɗa ‘Phase 3’ da ke jihar Kano.
Sadiya Muhammad, wacce aka fi sani da Sadiya Gyale, ta kasance ɗaya daga cikin taurarin da ke da basira wajen yin shiri mai kyau a kowane ɓangare aka saka ta a fim.
Tauraruwar ta yi baya da harkar fim ne bayan da aka yi aurenta na farko a shekarar 2015 da wani Barista Abubakar da ke aiki a jihar Kaduna. Sai dai auren bai jima ba, domin kuwa an yi ta samun saɓani da rashin fahimtar juna a tsakaninsu.
Kasancewar Baristan ya buƙaci kar a yaɗa bayanan auren nasu ga jama’a musamman a kafafen sadarwa, Sadiya ta watsa hotunan aurensu a shafukan sada zumunta, wanda a sanadiyar haka, Baristan ya danƙa mata takardar sake ta. Faruwar hakan ya sanya ta cikin bakin ciki tare da nesanta kanta daga jama’a da shiga harkar fim.
Sadiya, ta fito cikin fina-finai da dama da su ka haɗa da; gyale, ƴar fim, albashi, gidan gado, gwamnati, gwanaye, tutar so, gidan iko da dai sauransu.
Sabon auren nata ya sa al’umma da dama daga cikin masoya na yi mata fatan alkhairi da kuma addu’ar samun farin ciki a gidan.
