
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wa’adin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta yamma (ECOWAS), ya ƙare a ranar 7 ga watan Yuli, 2024.
Za a gudanar da taron ƙungiyar karo na 65 da aka saba yi, a fadar shugaban Nijeriya da ke Abuja inda a nan Tinubu zai miƙa ragamar shugabancin ECOWAS a hannun wanda zai gaje shi.
A watan Yulin 2023 ne aka zaɓi shugaba Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar a zamanta na 63 a Bissau, babban birnin ƙasar Guinea-Bissau.
