Shugabannin Mali, Burkina Faso da Niger sun ƙulla sabuwar haɗaka bayan ficewa daga ECOWAS

Spread the love

Shugabannin soja na ƙasashen Niger,Mali da Burkina Faso sun ƙulla wata sabuwar haɗaka bayan ficewa daga tarayyar ECOWAS.

Anyi wannan taron ne a babban birnin Niger, Niamey. Wannan haɗakar sun yi ta ne domin ƙarfafa alaƙa dake tsakanin kasashen ta ɓangaren tsaro da kuma tattalin arziki, wanda suka sanyawa suna “Alliance of Sahel State” (AES).

Wannan taron shine ma farko da dukkanin shugabannin ƙasashen uku suka haɗu tun bayar hawan kowannen su ƙaragar mulki. Kuma yana zuwa watanni uku da ficewar su daga tarayyar ECOWAS.

Tchiani, yayin magana a taron yace, ECOWAS ta zama barazana ga ƙasashen su, don haka dole ya sanya suka ƙulla wannan haɗaka ta ƙasashe wanda basu bin umarnin turawan yamma.

Wannan haɗakar ta zo ne a lokacin da ECOWAS ke shirin baban taron ta a birnin Abuja

By ukarofi