
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Babbar kotun jihar Legas ta umarci tsohuwar ministar ma’aikatar jinƙai da ci gaban ƙasa, Sadiya Farouk ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ta sarrafa Naira biliyan 729 ga talakawan Nijeriya miliyan 24.3 a cikin wata shida.
Cikin bayanan da kotun ta buƙaci tsohuwar ministar ta yi sun haɗa da; adadin waɗanda suka ci moriyar kuɗin, jihohin da aka bai wa kasafi da kuma nawa aka bai wa kowacce.
Alƙali Deinde Dipeolu ya yi hukuncin bayan da cibiyar tabbatar adalci da Mulki Nagari (SERAP) ta buƙaci a yi hakan ƙarƙashin dokar ƴancin sanarwa ta FHC/L/CS/853/2021.
Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya ce sun samu takardar asalin na hukuncin kotun ne a ranar juma’a da ta gabata.
Takardar wacce alƙalin ya rubuta ta ƙunshi bayanai kamar haka; ” wajibi ne a kan tsohuwar ministar ta yi bayani ga kowa har da SERAP, kamar yadda dokar sanarwa ta tanadar, don haka ina bada umarni ga ministar da ta yi cikakken bayanin yadda ta sarrafa Naira biliyan 729 ga talakawan Nijeriya miliyan 24.3 a shekarar 2021.
Sannan, Alƙalin ya umarce ta da yin bayanin hikimar biyan Naira 5,000 ga talakawan wanda hakan kashi 5 ne cikin kasafin kuɗin Nijeriya (Naira tiriliyan 13.6) na shekarar 2021.
Haka nan, ministar ta yi bayanin yadda aka zaɓi waɗanda suka ci moriyar kuɗin da kuma hanyoyin da ƙuɗaɗen suka kai gare su.
Dipeolu ya ƙara da cewa, Sadiya ba ta faɗi dalilin da ya sa ta ƙi yin cikakken bayani ga SERAP ba duk da cewa cibiyar ta nemi hakan, saboda haka ta fito da bayanan da ke buƙata daga gare ta.
Kazalika, Alƙalin ya yi watsi da neman ƙin sauraron ƙarar da wakilan ministar suka shigar inda ya fifita buƙatar SERAP a yayin hukunci kan lamarin.
