
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
‘Yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da sace wasu ƴan jarida biyu tare da iyalansu da aka yi a ranar Asabar da misalin ƙarfe 10:30 na dare.
Mai magana da yawun rundunar Mansir Hassan ya faɗi hakan a yayain wata hira da ‘News Agency of Nigeria’ inda ya ce jami’ansu na ƙoƙari wajen ganin an ceto su daga waɗanda suka yi garkuwa dasu wanda a yanzu haka an watsa tawagar ƴan sandan a yankunan da ake tsammanin suna nan.
Mansir ya ce, ɗaya da cikin su shi ne Abdulgafar Alabelewa, shugaban wakilan ‘Chapel’ na ƙungiyar ƴan jaridu (NUJ) reshen jihar kuma wakilin jaridar ‘The Nation’ tare da wasu ƴan gidansu guda uku da aka sace a yankin Danhono 2, Millennium City a Kaduna.
Sannan, sai wakilin jaridar ‘Blueprint’, Abdulraheem Aodo tare da matarsa.
