Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin Kotun Ƙoli kan cin gashin ƙananan hukumomi

Spread the love

Shugaba Tinubu yayi maraba da hukuncin kotun ƙolin a kan cin gashin kan ƙananan hukumomi

Shugaba Tinubu ya nuna murna ƙwarai dagaske a kan hukuncin da kotun ta yanke na ba ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu.

Wannan ya fito ne a wata sanarwa daga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar sadarwa, Ajuri Ngelale.

Ya bayyana cewa wannan hukuncin ya bayyana irin ƙudurin da gwamnatin sa ke da shi wajen ganin mun bi doka a tsarin gyaran da muka zo dashi”

Ya cigaba da cewa wannan ya zama dole saboda ƙananan ayyuka irin su saka fitilar titi, gyaran wasu tituna, tsaron unguwanni duk ya kamata ƙananan hukumomi su iya gudanar dasu.

Shugaban ya yaba wa ministan shari’a na ƙasa domin jajircewa wajen ganin an cimma wannan nasara. Ya cigaba da cewa, gwamnatinsa zata cigaba da kare hakkin yan najeriya.

By ukarofi