An karɓe ikon Sarkin Musulmi kan hakimansa

Spread the love

Majalisar Sarkin Musulmi sun cire masa ikon naɗa hakimai a jihar, yayin da Gwamna Aliyu Ahmed ya sanya hannu a dokar da ta ba da ikon haka.

Wannan dokar, ta cire wa sarkin Musulmin duk wani iko na naɗa hakimai da dagatai a faɗin Jihar Sokoto.

Yayin bikin ƙaddamar da dokar, gwaman yace ba anyi dokar bane don muzantawa wani, sai dai domin ƙarfafa mulkin dimukraɗiya a faɗin Jihar.

Ya cigaba da cewa, malamai da sarakunan gargajiya su daina bari yan siyasa suna amfani dasu wajen cin ma manufofinso na siyasa.

A ranar dai ya sanya hannu ga dokar da ta hana wariya ga mutane masu buƙatu na musamman, da dokar ƙasa, zakka da waƙafi.

By ukarofi