Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba da hukuncin da Kotun Ƙolin Nijeriya ta yanke a jiya, inda ta tabbatar da ‘yancin ƙananan hukumomi.
A sanarwar da fadar shugaban ta fitar bayan hukuncin a ranar Alhamis, shugaban ya ce hukuncin tamkar jaddada matsayin ƙaramar hukuma ne a kundin tsarin mulkin ƙasar.
A hukuncinta na ranar Alhamis, Kotun Ƙolin Nijeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.
Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya su ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu daga kason tarayya.
Shugaba Tinubu ya ce wannan mataki ne da ya tabbatar da matsayin ƙaramar hukuma a matsayin ɓangare na gwamnati da kuma tabbatar da shugabanci nagari.
Ya ce rashin sakin mara ga ƙananan hukumomi babbar matsala ce ga ci gaban ƙasa musamman yadda ba a jin tasirin gwamnati a karkara.
Shugaban ya jaddada cewa a yanzu ya zama wajibi kan shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da cewa ɗimbin ‘yan Nijeriya mazauna wannan matakin sun gamsu da cewa suna cin gajiyar ayyukan da suka shafi jama’a.
“Ajandar sabunta fata ta shafi al’ummar ƙasar nan, a kowane mataki, ba tare da la’akari da addini, ƙabila, jinsi, ɓangaranci, siyasa, ko wani layi na wucin gadi da suka ce akwai a tsakaninmu, ƙasar nan ta mu ce gabaɗaya. Wannan hukunci, al’ummarmu musamman talakawa za su iya yi wa shugabanninsu hisabi a kan abin da aka aika a asusun ƙananan hukumomi, kuma a yanzu a yi ayyuka ba tare da uzuri ba.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Mista Lateef Fagbemi (SAN) bisa jajircewarsa da kishin ƙasa kan wannan muhimmin aiki.
Shugaban ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta ci gaba da jajircewa wajen kare ƙa’idojin kundin tsarin mulkin ‘yan ƙasa, cibiyoyin gwamnati, hukumomin gwamnati domin ci gaba da gina ingantaccen tsarin gudanar da mulki wanda zai yi aiki ga kowane ɗan Nijeriya.
