Daga JOHN D. WADA, a LAFIYA
Ƙungiyar Cigaban Al’ummar Ƙabilar Tibi na Duniya, wadda da ake fi sani da MZOUGH U TIV, reshen jihar Nasarawa ta ƙaryata wani zargi da wata ƙungiyar ƙabilar Alago a jihar ta yi cewa ‘yan ƙabilar ta Tibi suna kai hare-hare da yi wa al’ummarsu ta Alago kwantan ɓauna a yankunan Ƙaramar Hukumar Keana a jihar.
Shugaban ƙungiyar ƙabilar Tibin na reshen jihar Nasarawa, Kwamared Philip Nongu ne ya bayyana haka a cikin wata takardar bayan taro wanda aka raba wa manema labarai a Lafiya fadar gwamnatin jihar ranar Laraba 10 ga watan Yulin shekarar 2024 da ake ciki.
Ya ce, ya zama wajibi ga ƙungiyar ta fito fili ta musanta zargin kasancewar dukka zargi da ‘yan ƙungiyar ƙabilar Alagon suka bayyana a sanarwar na su babu kamshin gaskiya balle mafaka.
Kwamared Philip Nongu ya kuma bayyana cewa, al’ummar ƙabilar Tibi a jihar dama duniya bakiɗaya kowa yasan su da son zaman lafiya da makwabtansu sauran ƙabilu daban-daban da ke zama da su a duk inda suke, kuma tun da suke rayuwa a wannan yankin aramar hukumar Keana da kewayen ta bakiɗaya ba su taɓa da da zaune tsaye ko kai wa wani hari kamar yadda ‘yan Alagon suka bayyana a sanarwar nasu ba.
Maimakon haka a cewarsa, sau da yawa al’ummar Alagon ne tare da haɗin kan wasu miyagun Fulani makiyaya ke cigaba da kashe musu mutane ba gaira ba dalili.
Philip Nongu ya ƙara da cewa, ko a ’yan kwanakin nan wasu sarakunan gargajiya tare da haɗin kan Fulanin daga wajen jihar sun yi ta kwace wa al’ummar su na Tibi da ke yankin ƙaramar hukumar Keana ɗin da sauran sassan jihar bakiɗaya filayen noman su da sauran su inda suke cewa sune ainihin masu ƙauyukan wai Tibin maki ne ba ’yan asalin jihar ta Nasarawa ba.
A cewarsa, duk da cewa tarihi ta bayyana ƙarara cewa al’ummar Tibi sun kwashe sama da shekaru aru-aru a waɗannan yankunan Keana da kewayen ta dama jihar bakiɗaya.
Har ila yau, Philip Nongu ya kuma bayyana takaicin sa a cikin takardar dangane da yadda a cewarsa a ’yan kwanakin nan wasu miyagun mutane ’yan ta’adda suna cigaba da kai wa al’ummar su ta Tibi hare-hare inda suna kashe musu mutane a cikin garin na Keana da kewayen ta ba tare da jami’an tsaro da ke wajen suna ɗaukan matakin kare rayukan su ba inda ya ƙara da cewa har sojoji ma da ke yankunan saudayawa idan aka kai musu hare-haren sukan sanar da sojojin amma basa ɗaukar mataki da ya dace.
Wakilin mu dai ya gano cewa a cikin takardar zargin ta farko da ’yan ƙungiyar al’ummar Alagon suka rubuto sun zargi al’ummar Tibin ne musamman waɗanda ke yankin na ƙaramar hukumar Keana a jihar cewa su suke kai hare-haren wa al’ummar su a kowanne lokaci inda suke kuma cigaba da ta da fitina a yankin.
