Jami’an hukumar FBI sun tabbatar da kashe wanda ake zargi da yunƙurin kashe tsohon Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump. Sunce sunyi nasarar kashe Thomas Mathew crook, ɗan shekara 20 daga Pennsylvania.
A farkon sanarwa da suka bayar, sun ƙi yadda su bayyana sunan wanda ake zargin. Saboda a cewar su lokacin suna ta bincike kuma basu shirya faɗan wanda ya aikata wannan laifin ba.
Sai dai yan sandan Pennsylvania sun tabbatar da cewa yanzu, suna da tabbacin cewa babu wani abu mai ban tsoro irin wannan da sake faruwa.
