Nijeriya ina mafita? – Daga Uncle Larabi

Spread the love

Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI (UNCLE LARABI)

Wallahil azim! Idan ba mu yi wasa ba zuwa ƙarshen shekarar nan (2024) komai zai sake yin tsada ne fiye da yadda yake tsada a yanzu. Idan kuma mu ka sake sakankancewa wallahi kafin Tinubu ya sauka daga mulki, wanda ya ke da rabon gani (Allah ya sa mu ma mu na da rabon ganin ƙarshen mulkin nasa da na wasu ma) za a sha wahala ba kaɗan ba ta hauhawar farashin kayan masarufi.

A yanzu da na ke rubutun nan, ko kun san farashin Dala ɗaya ya haura Naira 1545. Farashin kayan masarufi kowanne sai wuta yake yi a na bin sa da fetur. Yanzu haka taliya ta gida, IRS leda ɗaya ta tasamma Naira 1000. Leda ɗaya fa da Buhari ya zo ya same ta, ta waje ma, akan Naira 65 zuwa Naira 80, ya ce a na zaluntar mu a hakan. Shi ma ya tafi ya bar ta a Naira 300. Mu na ta jinjina maganar. Yanzu haka kwanon shinkafa ya tasamma Naira 5000 ta Hausa, wadda ake nomawa a ƙasarmu.

A hakan ma kuma ba tsayawa tsadar ta yi ba, ƙara cigaba ta ke yi tamkar wutar daji. A halin da ake ciki a Nijeriya, babu maganar Kudu ko Arewa, duk sanda ka sayi abu, idan ka koma sake siya za ka tarar an sake ƙara ma sa kuɗi ne.

Bayan wannan masifar ta matsalar tashin kayan masarufi yanzu kuma su na sake son Jefa mu matsalar fetur, don duk gidajen mai sun rufe su na so nan gaba kaɗan su yi ƙari. Mu kuma (‘yan Allah ya ba mu abin siya kawai) sai mu sake naɗe hannayenmu mu cigaba da siyen tsadar. Mun gwammace a junanmu na kusa-kusa mu yi ta jin haushin junanmu.

A wannan tsadar rayuwar fa yanzu akwai gidaje da yawa da sau ɗaya su ke iya cin abinci. Wasu sau ɗayan ma na neman ya gagare su.

Gaskiyar magana, duk wanda yake da hannu cikin jefa ƙasar nan cikin mawuyacin halin da ake ciki a yanzu, in sha Allahu sai Allah ya soya shi ba mai ba frypan. Alfarmar Manzo sallallahu alaihi wassalam, don ya yi sanadiyyar jefa miliyoyin mutane cikin masifa da bala’i.

A baya akwai abubuwa da yawa da talaka bai ma ɗauke su wasu ‘luɗuries’ abubuwa ba, amma yanzu sun fi ƙarfin mai kuɗin ma, indai ba wanda ya ci ya tada kai ba ne, irin waɗanda suka ba wa Naira miliyan 500,000,000 baya ko irin waɗanda su ka ba wa Naira biliyan ɗaya baya.

Waɗannan fa Ina magana ne a kan mutanen da a ke rayuwa da su, ba wai ’yan siyasa ba ko manyan ’yan kasuwa ko manyan ɓarayin gwamnati ba. Gaskiyar magana idan har talaka bai yi tunani da hankalinsa da basirarsa ba wajen nemar wa kansa mafita, to waɗannan mutanen ba za su samar da wani abu na jin daɗi ga talaka ba face ƙara jefa shi cikin masifa da bala’i da shiga cikin halin ha’u’la’i ba.

Asabar, 6 ga Yuli, 2024.

Uncle Larabi marubuci ne. Za a samun sa a 08065418892

By ukarofi