
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Majalisar Dattijai ta sanar da cire Sanata Mohammed Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu a matsayin mai tsawatarwa inda ta maye gurbinsa da Tahir Mungono da ke wakiltar Borno ta Arewa.
An samu hukuncin hakan ne a wani jawabi da kakakin majalisar, Goodwill Akpabio ya yi ta wata ɗaukar murya wanda jiga-jigan mambobin APC da ke majalisar suka amince da hakan.
Majalisar ta yi hukuncin ne la’akari da sukan gwamnatin shugaba Tinubu da Ndume ya ke yi a ƴan kwanakin nan wanda hakan ya sa APC ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Umar Ganduje, ta aika da saƙo ga majalisar kan cewa Ndume ya sauka daga muƙaminsa, sannan ya sauya zuwa wata jam’iyyar da ya ke so.
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu sanatoci da ke biyayya ga shugaba Tinubu ne suka kimtsa yadda za a tuɓe Ndume daga muƙamin nasa tare da dakatar da shi kamar yadda aka yi wa Sanata Abdul Ningi da ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya.
Abdul Ningi shi ne wanda BBC ta yi hira da shi a watan Maris inda ya ce an ware Naira tiriliyan 3.7 cikin kasafin kuɗin ƙasa da ba a faɗi abin da aka yi da su ba wanda hakan ya sa aka dakatar da shi na wata uku a Majalisa
