Da ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Nijeriya yayin da ya alƙawuranta sabonta dokar albashi duk bayan shekaru uku.

Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya faɗi hakan a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a ranar Alhamis.

Ministan ya ce, shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a yayin ganawa da shugabannin haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago.

Waɗanda su ka halarci zaman sun haɗa da shugaban ƙungiyar ƙwadago (NLC), Joe Ajaero da na ƙungiyar kasuwanci (TUC), Festus Usifo tare da wasu mambobin ƙungiyoyin.

Kafin zaman, ƙungiyar ƙwadago ta haƙiƙance kan Naira 250,000.

By Babaji