Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin cewa ɗalibai da ba su kai shekaru 18 ba su cancanci shiga manyan makarantu a Najeriya ba.
Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya sanar da wannan umarni a Abuja. A jawabinsa na bude taron gurbin karatu na 2024 da hukumar JAMB ta shirya.
Ya kuma umarci hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB da ta aiwatar da sabbin ƙa’idojin da suka fara daga shekarar 2024.
Ya ce matakin ya yi daidai da shawarwarin hukumar kula da ilimi ta kasa (NCE) da wasu dokoki, daga yanzu ya kamata a bi umarnin.
Ya ce: “Na kasance shugaban jami’a tsawon shekaru bakwai. Ina da bayanai yadda waɗannan ɗalibai masu karancin shekaru ke kokawa ta hanyoyi da dama a duk lokacin da aka tura su cikin wadannan jami’o’in da wuri.”
