
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Babbar kotun tarayya da ke jihar Legas ta kori ƙarar da cibiyar tabbatar da ƴanci da adalci (SERAP), ta shigar wanda ke ƙalubalantar umarnin ofishin shugaban ƙasa na cewa a rufe layukan da ba a sadar da su da lambobin katin ɗan ƙasa ba (NIN).
Mai Shari’a Yelim Bogoro ya ce tsarin gwamnatin tarayya da ya buƙaci sadar da layuka da lambobin katin ɗan ƙasa ya tabbatar da cewa maslahar ƙasa amfani ne gare ta, don haka tana sama da dukkan ƴancin kowaye a ƙasar.
Waɗanda takardar ƙarar ta zayyano sun haɗa da; shugaban ƙasa, Antoni Janar da kuma Hukumar Sadarwa ta ƙasa (NCC), SERAP ta ce umarnin dakatar da layukan ƴan ƙasa sama da miliyan 72, tauye musu haƙƙi ne wanda ya saɓa wa ƴancinsu kamar yadda ya ke a dokar ƙasa.
A lokacin da ya ke jawabi, mai bai wa shugaban ƙasa shawara, Akintola Makinde ya ce babu ɗaya daga cikin ƴancin da SERAP ta yi ƙalubale a kai da ya ke dai-dai, sai dai umarnin da shugaban ƙasa ya bayar, ya samu goyon bayan sakin layi na 14(2)(b) da na 45 kamar yadda ya ke a dokar ƙasa.Makinde ya ƙara da cewa, an bada umarnin ne saboda ƙaruwar matsalolin tsaro, garkuwa da mutane a Nijeriya.
